Quran with Hausa translation - Surah An-Nisa’ ayat 24 - النِّسَاء - Page - Juz 5
﴿۞ وَٱلۡمُحۡصَنَٰتُ مِنَ ٱلنِّسَآءِ إِلَّا مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۖ كِتَٰبَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ وَأُحِلَّ لَكُم مَّا وَرَآءَ ذَٰلِكُمۡ أَن تَبۡتَغُواْ بِأَمۡوَٰلِكُم مُّحۡصِنِينَ غَيۡرَ مُسَٰفِحِينَۚ فَمَا ٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِهِۦ مِنۡهُنَّ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةٗۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا تَرَٰضَيۡتُم بِهِۦ مِنۢ بَعۡدِ ٱلۡفَرِيضَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا ﴾
[النِّسَاء: 24]
﴿والمحصنات من النساء إلا ما ملكت أيمانكم كتاب الله عليكم وأحل لكم﴾ [النِّسَاء: 24]
Abubakar Mahmood Jummi Da tsararrun auren* wasu maza, face dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littafin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nema da dukiyoyinku, kuna masu yin aure, ba masu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku ba su ijarorinsu bisa farillar sadaki. Babu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya** da shi a bayan farillar sadaki. Lalle ne Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima |
Abubakar Mahmoud Gumi Da tsararrun auren wasu maza, face dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littafin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nema da dukiyoyinku, kuna masu yin aure, ba masu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku ba su ijarorinsu bisa farillar sadaki. Babu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya da shi a bayan farillar sadaki. Lalle ne Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima |
Abubakar Mahmoud Gumi Da tsararrun auren wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya da shi a bãyan farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima |