Quran with Hausa translation - Surah Al-Fath ayat 11 - الفَتح - Page - Juz 26
﴿سَيَقُولُ لَكَ ٱلۡمُخَلَّفُونَ مِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ شَغَلَتۡنَآ أَمۡوَٰلُنَا وَأَهۡلُونَا فَٱسۡتَغۡفِرۡ لَنَاۚ يَقُولُونَ بِأَلۡسِنَتِهِم مَّا لَيۡسَ فِي قُلُوبِهِمۡۚ قُلۡ فَمَن يَمۡلِكُ لَكُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔا إِنۡ أَرَادَ بِكُمۡ ضَرًّا أَوۡ أَرَادَ بِكُمۡ نَفۡعَۢاۚ بَلۡ كَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرَۢا ﴾
[الفَتح: 11]
﴿سيقول لك المخلفون من الأعراب شغلتنا أموالنا وأهلونا فاستغفر لنا يقولون بألسنتهم﴾ [الفَتح: 11]
Abubakar Mahmood Jummi Waɗanda aka bari daga ƙauyawa* za su ce maka, "Dukiyoyinmu da iyalanmu sun shagaltar da mu, sai ka nema mana gafara." Suna faɗa, da harsunansu, abin da ba shi ne a cikin zukatansu ba. Kace: "To, wane ne ke mallakar wani abu daga Allah saboda ku, idan Ya yi nufin wata cuta agare ku ko kuma (idan) Ya yi nufin wani amfani a gare ku? A'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗanda aka bari daga ƙauyawa za su ce maka, "Dukiyoyinmu da iyalanmu sun shagaltar da mu, sai ka nema mana gafara." Suna faɗa, da harsunansu, abin da ba shi ne a cikin zukatansu ba. Kace: "To, wane ne ke mallakar wani abu daga Allah saboda ku, idan Ya yi nufin wata cuta agare ku ko kuma (idan) Ya yi nufin wani amfani a gare ku? A'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa zã su ce maka, "Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara." Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: "To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma (idan) Ya yi nufin wani amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatãwa |