Quran with Hausa translation - Surah Al-hadid ayat 20 - الحدِيد - Page - Juz 27
﴿ٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا لَعِبٞ وَلَهۡوٞ وَزِينَةٞ وَتَفَاخُرُۢ بَيۡنَكُمۡ وَتَكَاثُرٞ فِي ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَوۡلَٰدِۖ كَمَثَلِ غَيۡثٍ أَعۡجَبَ ٱلۡكُفَّارَ نَبَاتُهُۥ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَىٰهُ مُصۡفَرّٗا ثُمَّ يَكُونُ حُطَٰمٗاۖ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٞ شَدِيدٞ وَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٞۚ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ ﴾
[الحدِيد: 20]
﴿اعلموا أنما الحياة الدنيا لعب ولهو وزينة وتفاخر بينكم وتكاثر في الأموال﴾ [الحدِيد: 20]
Abubakar Mahmood Jummi Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakaninku da gasar wadata ta dukiya da ɗiya, kamar misalin shuka wadda yabanyarta ta bayar da sha'awa ga manoma, sa'an nan ta ƙeƙashe, har ka ganta ta zama rawaya sa'an nan ta koma rauno. Kuma, alamra akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da yarda. Kuma rayuwar duniya ba ta zama ba face ɗan jin daɗin ruɗi kawai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakaninku da gasar wadata ta dukiya da ɗiya, kamar misalin shuka wadda yabanyarta ta bayar da sha'awa ga manoma, sa'an nan ta ƙeƙashe, har ka ganta ta zama rawaya sa'an nan ta koma rauno. Kuma, alamra akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da yarda. Kuma rayuwar duniya ba ta zama ba face ɗan jin daɗin ruɗi kawai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ku sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai |