Quran with Hausa translation - Surah Al-An‘am ayat 148 - الأنعَام - Page - Juz 8
﴿سَيَقُولُ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ لَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَآ أَشۡرَكۡنَا وَلَآ ءَابَآؤُنَا وَلَا حَرَّمۡنَا مِن شَيۡءٖۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ حَتَّىٰ ذَاقُواْ بَأۡسَنَاۗ قُلۡ هَلۡ عِندَكُم مِّنۡ عِلۡمٖ فَتُخۡرِجُوهُ لَنَآۖ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا تَخۡرُصُونَ ﴾
[الأنعَام: 148]
﴿سيقول الذين أشركوا لو شاء الله ما أشركنا ولا آباؤنا ولا حرمنا﴾ [الأنعَام: 148]
Abubakar Mahmood Jummi Waɗanda suka yi shirki* za su ce: "Da Allah Ya so da ba mu yi shirki ba, kuma da ubanninmu ba su yi ba, kuma da ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutanen da suke a gabaninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azabarMu. Ka ce: "Shin, kuna da wani ilmi a wurinku domin ku fito mana da shi? Ba ku bin kome face zato kuma ba ku zama ba face ƙiri-faɗi kawai kuke yi |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗanda suka yi shirki za su ce: "Da Allah Ya so da ba mu yi shirki ba, kuma da ubanninmu ba su yi ba, kuma da ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutanen da suke a gabaninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azabarMu. Ka ce: "Shin, kuna da wani ilmi a wurinku domin ku fito mana da shi? Ba ku bin kome face zato kuma ba ku zama ba face ƙiri-faɗi kawai kuke yi |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗanda suka yi shirki zã su ce: "Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi |