Quran with Hausa translation - Surah Al-An‘am ayat 93 - الأنعَام - Page - Juz 7
﴿وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمۡ يُوحَ إِلَيۡهِ شَيۡءٞ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثۡلَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّٰلِمُونَ فِي غَمَرَٰتِ ٱلۡمَوۡتِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ بَاسِطُوٓاْ أَيۡدِيهِمۡ أَخۡرِجُوٓاْ أَنفُسَكُمُۖ ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَكُنتُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهِۦ تَسۡتَكۡبِرُونَ ﴾
[الأنعَام: 93]
﴿ومن أظلم ممن افترى على الله كذبا أو قال أوحي إلي ولم﴾ [الأنعَام: 93]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, ko kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhali kuwa ba a yi wahayin kome ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misalin abin da Allah Ya saukar?" Kuma da ka gani, a lokacin da azzalumai suke cikin mayen mutuwa, kuma mala'iku suna masu shimfiɗa hannuwansu, (suna ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau ana saka muku da azabar wulaƙanci saboda abin da kuka kasance kuna faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ayoyinSa kuna yin girman kai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, ko kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhali kuwa ba a yi wahayin kome ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misalin abin da Allah Ya saukar?" Kuma da ka gani, a lokacin da azzalumai suke cikin mayen mutuwa, kuma mala'iku suna masu shimfiɗa hannuwansu, (suna ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau ana saka muku da azabar wulaƙanci saboda abin da kuka kasance kuna faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ayoyinSa kuna yin girman kai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai |