Quran with Hausa translation - Surah At-Taubah ayat 107 - التوبَة - Page - Juz 11
﴿وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مَسۡجِدٗا ضِرَارٗا وَكُفۡرٗا وَتَفۡرِيقَۢا بَيۡنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَإِرۡصَادٗا لِّمَنۡ حَارَبَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ مِن قَبۡلُۚ وَلَيَحۡلِفُنَّ إِنۡ أَرَدۡنَآ إِلَّا ٱلۡحُسۡنَىٰۖ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ ﴾
[التوبَة: 107]
﴿والذين اتخذوا مسجدا ضرارا وكفرا وتفريقا بين المؤمنين وإرصادا لمن حارب الله﴾ [التوبَة: 107]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma waɗanda* suka riƙi wani masallaci domin cuta da kafirci da neman rarrabewa a tsakanin muminai da fakewa ga taimakon wanda ya yaƙi Allah da ManzonSa daga gabani, kuma haƙiƙa suna yin rantsuwa cewa, "Ba mu yi nufin komai ba face alheri", alhali kuwa Allah Yana yin shaida cewa, su, haƙiƙa, maƙaryata ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma waɗanda suka riƙi wani masallaci domin cuta da kafirci da neman rarrabewa a tsakanin muminai da fakewa ga taimakon wanda ya yaƙi Allah da ManzonSa daga gabani, kuma haƙiƙa suna yin rantsuwa cewa, "Ba mu yi nufin komai ba face alheri", alhali kuwa Allah Yana yin shaida cewa, su, haƙiƙa, maƙaryata ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma waɗanda suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa, su, haƙĩƙa, maƙaryata ne |