×

Surah As-Saff in Hausa

Quran Hausa ⮕ Surah Saff

Translation of the Meanings of Surah Saff in Hausa - الهوسا

The Quran in Hausa - Surah Saff translated into Hausa, Surah As-Saff in Hausa. We provide accurate translation of Surah Saff in Hausa - الهوسا, Verses 14 - Surah Number 61 - Page 551.

بسم الله الرحمن الرحيم

سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (1)
Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah alhãli kuwa, Shi ne Mabuwayi, Mai hikima
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفْعَلُونَ (2)
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Don me kuke faɗin abin dã ba ku aikatãwa
كَبُرَ مَقْتًا عِندَ اللَّهِ أَن تَقُولُوا مَا لَا تَفْعَلُونَ (3)
Ya girma ga zama abin ƙyãma awurin Allah, ku faɗi abin da bã ku aikatãwa
إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الَّذِينَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِهِ صَفًّا كَأَنَّهُم بُنْيَانٌ مَّرْصُوصٌ (4)
Lalle Allah Yanã son waɗanda ke yin yãƙi dõmin ɗaukaka Kalmar Sa, a cikin safu kamar sũ gini ne mai ɗamfarar jũna
وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ يَا قَوْمِ لِمَ تُؤْذُونَنِي وَقَد تَّعْلَمُونَ أَنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ ۖ فَلَمَّا زَاغُوا أَزَاغَ اللَّهُ قُلُوبَهُمْ ۚ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ (5)
Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Alah ne zuwa gare ku?" To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai
وَإِذْ قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُم مُّصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيَّ مِنَ التَّوْرَاةِ وَمُبَشِّرًا بِرَسُولٍ يَأْتِي مِن بَعْدِي اسْمُهُ أَحْمَدُ ۖ فَلَمَّا جَاءَهُم بِالْبَيِّنَاتِ قَالُوا هَٰذَا سِحْرٌ مُّبِينٌ (6)
Kuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryama ya ce: "Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke zuwa a bãyãna, Sũnansa Ahmad (Mashãyabo)." To, a lõkacin da ya jẽ musu da hujjõji, suka ce: "Wannan sihiri ne, bayyananne
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ وَهُوَ يُدْعَىٰ إِلَى الْإِسْلَامِ ۚ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ (7)
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya Jingina ta ga Allah, alhãli kuwa shĩ, anã kiran sa zuwa ga Musulunci? Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai
يُرِيدُونَ لِيُطْفِئُوا نُورَ اللَّهِ بِأَفْوَاهِهِمْ وَاللَّهُ مُتِمُّ نُورِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ (8)
Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunansu alhãli kuwa Allah Mai kammala hasken Sa ne, kuma kõ da kãfirai sun ƙi
هُوَ الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالْهُدَىٰ وَدِينِ الْحَقِّ لِيُظْهِرَهُ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُشْرِكُونَ (9)
Shi ne wanda Ya aiko Manzon Sa da shiriya da addĩnin gakiya, dõmin Ya ɗaukaka shi a kan wani addĩni dukansa kuma kõ dã mushirikai sun ƙi
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَىٰ تِجَارَةٍ تُنجِيكُم مِّنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ (10)
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Shin, in nũna muku wani fatauci wanda zai tsarshe ku daga wata azãba mai raɗaɗi
تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَتُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ بِأَمْوَالِكُمْ وَأَنفُسِكُمْ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ (11)
Ku yi ĩmani da Allah da Manzon Sa, kuma ku yi jihãdi ga ɗaukaka kalmar Allah game da dũkiyõyinku da rãyukanku. Wannan shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna da sani
يَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَيُدْخِلْكُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ وَمَسَاكِنَ طَيِّبَةً فِي جَنَّاتِ عَدْنٍ ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (12)
Sai Allah Ya gãfarta muku zunubbanku, kuma Ya shigar da ku gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, da waɗansu ɗãkuna mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar zama. Wannan shĩ ne babban rabo, mai girma
وَأُخْرَىٰ تُحِبُّونَهَا ۖ نَصْرٌ مِّنَ اللَّهِ وَفَتْحٌ قَرِيبٌ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ (13)
Da wata (falala) da yake kunã son ta; taimako daga Allah da cin nasara wanda yake kusa. Kuma ka yi bushãra ga mũminai
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا أَنصَارَ اللَّهِ كَمَا قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ لِلْحَوَارِيِّينَ مَنْ أَنصَارِي إِلَى اللَّهِ ۖ قَالَ الْحَوَارِيُّونَ نَحْنُ أَنصَارُ اللَّهِ ۖ فَآمَنَت طَّائِفَةٌ مِّن بَنِي إِسْرَائِيلَ وَكَفَرَت طَّائِفَةٌ ۖ فَأَيَّدْنَا الَّذِينَ آمَنُوا عَلَىٰ عَدُوِّهِمْ فَأَصْبَحُوا ظَاهِرِينَ (14)
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Ĩsã ɗanMaryama ya ce ga Hawãriyãwa, "Waɗanne ne mataimakãna zuwa ga (aikin) Allah?" Sai wata ƙungiya daga Banĩ Isrã'ĩla ta yi ĩmãni, kuma wata ƙungiya ta kãfirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi ĩmãni a kan maƙiyansu, sabõda haka suka wãyi gari marinjãya
❮ Previous Next ❯

Surahs from Quran :

1- Fatiha2- Baqarah
3- Al Imran4- Nisa
5- Maidah6- Anam
7- Araf8- Anfal
9- Tawbah10- Yunus
11- Hud12- Yusuf
13- Raad14- Ibrahim
15- Hijr16- Nahl
17- Al Isra18- Kahf
19- Maryam20- TaHa
21- Anbiya22- Hajj
23- Muminun24- An Nur
25- Furqan26- Shuara
27- Naml28- Qasas
29- Ankabut30- Rum
31- Luqman32- Sajdah
33- Ahzab34- Saba
35- Fatir36- Yasin
37- Assaaffat38- Sad
39- Zumar40- Ghafir
41- Fussilat42- shura
43- Zukhruf44- Ad Dukhaan
45- Jathiyah46- Ahqaf
47- Muhammad48- Al Fath
49- Hujurat50- Qaf
51- zariyat52- Tur
53- Najm54- Al Qamar
55- Rahman56- Waqiah
57- Hadid58- Mujadilah
59- Al Hashr60- Mumtahina
61- Saff62- Jumuah
63- Munafiqun64- Taghabun
65- Talaq66- Tahrim
67- Mulk68- Qalam
69- Al-Haqqah70- Maarij
71- Nuh72- Jinn
73- Muzammil74- Muddathir
75- Qiyamah76- Insan
77- Mursalat78- An Naba
79- Naziat80- Abasa
81- Takwir82- Infitar
83- Mutaffifin84- Inshiqaq
85- Buruj86- Tariq
87- Al Ala88- Ghashiya
89- Fajr90- Al Balad
91- Shams92- Lail
93- Duha94- Sharh
95- Tin96- Al Alaq
97- Qadr98- Bayyinah
99- Zalzalah100- Adiyat
101- Qariah102- Takathur
103- Al Asr104- Humazah
105- Al Fil106- Quraysh
107- Maun108- Kawthar
109- Kafirun110- Nasr
111- Masad112- Ikhlas
113- Falaq114- An Nas