| حم (1) Ḥ. M̃
 | 
| وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ (2) Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani
 | 
| إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ (3) Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi
 | 
| فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ (4) A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne
 | 
| أَمْرًا مِّنْ عِندِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ (5) Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã
 | 
| رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ (6) Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani
 | 
| رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ (7) (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka)
 | 
| لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ (8) Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko
 | 
| بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَ (9) A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka
 | 
| فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍ (10) Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne
 | 
| يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ (11) Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi
 | 
| رَّبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ (12) Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne
 | 
| أَنَّىٰ لَهُمُ الذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ (13) Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)
 | 
| ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ (14) Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa* ne, mahaukaci
 | 
| إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَ (15) Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin)
 | 
| يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَىٰ إِنَّا مُنتَقِمُونَ (16) Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne
 | 
| ۞ وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ (17) Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu
 | 
| أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ (18) (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku
 | 
| وَأَن لَّا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي آتِيكُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ (19) Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne
 | 
| وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ (20) Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni
 | 
| وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ (21) Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni
 | 
| فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَٰؤُلَاءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ (22) Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi
 | 
| فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ (23) (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku)
 | 
| وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ (24) Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa
 | 
| كَمْ تَرَكُوا مِن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ (25) Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari
 | 
| وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ (26) Da shuke-shuke da matsayi mai kyau
 | 
| وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ (27) Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu
 | 
| كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَ (28) Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam
 | 
| فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَ (29) Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka *a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba
 | 
| وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ (30) Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa
 | 
| مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِّنَ الْمُسْرِفِينَ (31) Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna
 | 
| وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ (32) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne
 | 
| وَآتَيْنَاهُم مِّنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاءٌ مُّبِينٌ (33) Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna
 | 
| إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَيَقُولُونَ (34) Lalle waɗannan mutãne*, haƙĩka, sunã cẽwa
 | 
| إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ (35) Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba
 | 
| فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (36) Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya
 | 
| أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ (37) shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi
 | 
| وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ (38) Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã
 | 
| مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ (39) Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba
 | 
| إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ (40) Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya
 | 
| يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ (41) Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba
 | 
| إِلَّا مَن رَّحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ (42) fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
 | 
| إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِ (43) Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã)
 | 
| طَعَامُ الْأَثِيمِ (44) Ita ce abincin mai laifi
 | 
| كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ (45) Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna
 | 
| كَغَلْيِ الْحَمِيمِ (46) Kamar tafasar ruwan zãfi
 | 
| خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ (47) (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm
 | 
| ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ (48) Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi
 | 
| ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ (49) (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma
 | 
| إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ (50) Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi
 | 
| إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍ (51) Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce
 | 
| فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ (52) A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari
 | 
| يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَ (53) Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna
 | 
| كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ (54) Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyawun idãnu, mãsu girmansu
 | 
| يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَ (55) Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro)
 | 
| لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ (56) Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm
 | 
| فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (57) Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma
 | 
| فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ (58) Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa
 | 
| فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ (59) Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne
 |