القرآن باللغة الهوسا - سورة الزلزلة مترجمة إلى اللغة الهوسا، Surah Zalzalah in Hausa. نوفر ترجمة دقيقة سورة الزلزلة باللغة الهوسا - Hausa, الآيات 8 - رقم السورة 99 - الصفحة 599.
إِذَا زُلْزِلَتِ الْأَرْضُ زِلْزَالَهَا (1) Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta |
وَأَخْرَجَتِ الْأَرْضُ أَثْقَالَهَا (2) Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi |
وَقَالَ الْإِنسَانُ مَا لَهَا (3) Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta |
يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا (4) A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta |
بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَىٰ لَهَا (5) cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta |
يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتًا لِّيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ (6) A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu |
فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ (7) To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi |
وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ (8) Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi |