اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ (1) Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta |
خَلَقَ الْإِنسَانَ مِنْ عَلَقٍ (2) Ya hahitta mutum daga gudan jini |
اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ (3) Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci |
الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ (4) Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami |
عَلَّمَ الْإِنسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ (5) Ya sanar da mutum abin da bai sani ba |
كَلَّا إِنَّ الْإِنسَانَ لَيَطْغَىٰ (6) A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu) |
أَن رَّآهُ اسْتَغْنَىٰ (7) Dõmin yã ga kansa, yã wadãta |
إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ الرُّجْعَىٰ (8) Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take |
أَرَأَيْتَ الَّذِي يَنْهَىٰ (9) Shin, kã ga wanda ke hana |
عَبْدًا إِذَا صَلَّىٰ (10) Bãwã idan yã yi salla |
أَرَأَيْتَ إِن كَانَ عَلَى الْهُدَىٰ (11) Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya |
أَوْ أَمَرَ بِالتَّقْوَىٰ (12) Ko ya yi umurni da taƙawa |
أَرَأَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ (13) Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya |
أَلَمْ يَعْلَم بِأَنَّ اللَّهَ يَرَىٰ (14) Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani |
كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًا بِالنَّاصِيَةِ (15) A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa |
نَاصِيَةٍ كَاذِبَةٍ خَاطِئَةٍ (16) Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi |
فَلْيَدْعُ نَادِيَهُ (17) Sai ya kirayi ƙungiyarsa |
سَنَدْعُ الزَّبَانِيَةَ (18) Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma) |
كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَاسْجُدْ وَاقْتَرِب ۩ (19) A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka) |