هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ (1) Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka |
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَاشِعَةٌ (2) Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne |
عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ (3) Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya |
تَصْلَىٰ نَارًا حَامِيَةً (4) Zã su shiga wata wuta mai zãfi |
تُسْقَىٰ مِنْ عَيْنٍ آنِيَةٍ (5) Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa |
لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ (6) Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi |
لَّا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِي مِن جُوعٍ (7) Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba |
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ (8) Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne |
لِّسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ (9) Game da aikinsu, masu yarda ne |
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ (10) (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya |
لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَاغِيَةً (11) Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta |
فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ (12) A cikinta akwai marmaro mai gudãna |
فِيهَا سُرُرٌ مَّرْفُوعَةٌ (13) A cikinta akwai gadãje maɗaukaka |
وَأَكْوَابٌ مَّوْضُوعَةٌ (14) Da kõfuna ar'aje |
وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ (15) Da filõli* jẽre |
وَزَرَابِيُّ مَبْثُوثَةٌ (16) Da katifu shimfiɗe |
أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ (17) Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su |
وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ (18) Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta |
وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ (19) Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su |
وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ (20) Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta |
فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنتَ مُذَكِّرٌ (21) sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai |
لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ (22) Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba |
إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ (23) Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta |
فَيُعَذِّبُهُ اللَّهُ الْعَذَابَ الْأَكْبَرَ (24) To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma |
إِنَّ إِلَيْنَا إِيَابَهُمْ (25) Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take |
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُم (26) Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi |