وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الْبُرُوجِ (1) Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara |
وَالْيَوْمِ الْمَوْعُودِ (2) Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa |
وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ (3) Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta* a cikinsa |
قُتِلَ أَصْحَابُ الْأُخْدُودِ (4) An la'ani mutãnen rãmi |
النَّارِ ذَاتِ الْوَقُودِ (5) Wato wuta wadda aka hura |
إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ (6) A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune |
وَهُمْ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ بِالْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ (7) Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce |
وَمَا نَقَمُوا مِنْهُمْ إِلَّا أَن يُؤْمِنُوا بِاللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ (8) Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa |
الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَاللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ (9) Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake |
إِنَّ الَّذِينَ فَتَنُوا الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ الْحَرِيقِ (10) Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara |
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْكَبِيرُ (11) Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba |
إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ (12) Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai |
إِنَّهُ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ (13) Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa) |
وَهُوَ الْغَفُورُ الْوَدُودُ (14) Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya |
ذُو الْعَرْشِ الْمَجِيدُ (15) Mai Al'arshi mai girma |
فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ (16) Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi |
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْجُنُودِ (17) Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka |
فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ (18) Fir'auna da samũdãwa |
بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي تَكْذِيبٍ (19) Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa |
وَاللَّهُ مِن وَرَائِهِم مُّحِيطٌ (20) Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa) |
بَلْ هُوَ قُرْآنٌ مَّجِيدٌ (21) Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma |
فِي لَوْحٍ مَّحْفُوظٍ (22) A cikin Allo tsararre |