سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى (1) Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka |
الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ (2) Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar |
وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ (3) Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri) |
وَالَّذِي أَخْرَجَ الْمَرْعَىٰ (4) Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã |
فَجَعَلَهُ غُثَاءً أَحْوَىٰ (5) Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa |
سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰ (6) Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba |
إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰ (7) Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye |
وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰ (8) Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi |
فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ الذِّكْرَىٰ (9) Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni |
سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَىٰ (10) Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna |
وَيَتَجَنَّبُهَا الْأَشْقَى (11) Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta |
الَّذِي يَصْلَى النَّارَ الْكُبْرَىٰ (12) Wanda zai shiga wutar da tã fi girma |
ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ (13) Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba |
قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّىٰ (14) Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo |
وَذَكَرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّىٰ (15) Kuma ya ambaci sũnan* Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla |
بَلْ تُؤْثِرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا (16) Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya |
وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ (17) Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa |
إِنَّ هَٰذَا لَفِي الصُّحُفِ الْأُولَىٰ (18) Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko |
صُحُفِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰ (19) Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã |