إِذَا وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ (1) Idan mai aukuwa ta auku |
لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ (2) Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta |
خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ (3) (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa |
إِذَا رُجَّتِ الْأَرْضُ رَجًّا (4) Idan aka girgiza ƙasã girgizwa |
وَبُسَّتِ الْجِبَالُ بَسًّا (5) Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa |
فَكَانَتْ هَبَاءً مُّنبَثًّا (6) Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa |
وَكُنتُمْ أَزْوَاجًا ثَلَاثَةً (7) Kuma kun kasance nau'i uku |
فَأَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ (8) Watau mazõwa dãma*. Mẽne ne mazõwa dãma |
وَأَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ (9) Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu |
وَالسَّابِقُونَ السَّابِقُونَ (10) Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan |
أُولَٰئِكَ الْمُقَرَّبُونَ (11) Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar |
فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ (12) A ckin Aljannar ni'ima |
ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَ (13) Jama'a ne daga mutãnen farko |
وَقَلِيلٌ مِّنَ الْآخِرِينَ (14) Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe |
عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ (15) (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu |
مُّتَّكِئِينَ عَلَيْهَا مُتَقَابِلِينَ (16) Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna |
يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُّخَلَّدُونَ (17) Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu |
بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ (18) Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga |
لَّا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنزِفُونَ (19) Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa |
وَفَاكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ (20) Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe |
وَلَحْمِ طَيْرٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ (21) Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa |
وَحُورٌ عِينٌ (22) Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu |
كَأَمْثَالِ اللُّؤْلُؤِ الْمَكْنُونِ (23) Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye |
جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (24) A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa |
لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًا (25) Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi |
إِلَّا قِيلًا سَلَامًا سَلَامًا (26) Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun |
وَأَصْحَابُ الْيَمِينِ مَا أَصْحَابُ الْيَمِينِ (27) Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma |
فِي سِدْرٍ مَّخْضُودٍ (28) (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya |
وَطَلْحٍ مَّنضُودٍ (29) Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya |
وَظِلٍّ مَّمْدُودٍ (30) Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya |
وَمَاءٍ مَّسْكُوبٍ (31) Da wani ruwa mai gudãna |
وَفَاكِهَةٍ كَثِيرَةٍ (32) Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa |
لَّا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍ (33) Bã su yankẽwa kuma bã a hana su |
وَفُرُشٍ مَّرْفُوعَةٍ (34) Da wasu shimfiɗu maɗaukaka |
إِنَّا أَنشَأْنَاهُنَّ إِنشَاءً (35) Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa |
فَجَعَلْنَاهُنَّ أَبْكَارًا (36) Sa'an nan Muka sanya su budurwai |
عُرُبًا أَتْرَابًا (37) Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya |
لِّأَصْحَابِ الْيَمِينِ (38) Ga mazõwa dãma |
ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَ (39) Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko |
وَثُلَّةٌ مِّنَ الْآخِرِينَ (40) Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe |
وَأَصْحَابُ الشِّمَالِ مَا أَصْحَابُ الشِّمَالِ (41) Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu |
فِي سَمُومٍ وَحَمِيمٍ (42) Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi |
وَظِلٍّ مِّن يَحْمُومٍ (43) Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi |
لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ (44) Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba |
إِنَّهُمْ كَانُوا قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَ (45) Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi |
وَكَانُوا يُصِرُّونَ عَلَى الْحِنثِ الْعَظِيمِ (46) Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma |
وَكَانُوا يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ (47) Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan |
أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ (48) Shin, kuma da ubanninmu na farko |
قُلْ إِنَّ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ (49) Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe |
لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَاتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ (50) Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne |
ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا الضَّالُّونَ الْمُكَذِّبُونَ (51) Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa |
لَآكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ (52) Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã) |
فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ (53) Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta |
فَشَارِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ الْحَمِيمِ (54) Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi |
فَشَارِبُونَ شُرْبَ الْهِيمِ (55) Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa |
هَٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ الدِّينِ (56) Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako |
نَحْنُ خَلَقْنَاكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَ (57) Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba |
أَفَرَأَيْتُم مَّا تُمْنُونَ (58) Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi |
أَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُ أَمْ نَحْنُ الْخَالِقُونَ (59) Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa |
نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ الْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ (60) Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa* ba |
عَلَىٰ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَالَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِي مَا لَا تَعْلَمُونَ (61) A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba |
وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ النَّشْأَةَ الْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَ (62) Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba |
أَفَرَأَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَ (63) Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa |
أَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُ أَمْ نَحْنُ الزَّارِعُونَ (64) Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa |
لَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَاهُ حُطَامًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَ (65) Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki |
إِنَّا لَمُغْرَمُونَ (66) (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra |
بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ (67) Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa |
أَفَرَأَيْتُمُ الْمَاءَ الَّذِي تَشْرَبُونَ (68) Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha |
أَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ الْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ الْمُنزِلُونَ (69) Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa |
لَوْ نَشَاءُ جَعَلْنَاهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَ (70) Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa |
أَفَرَأَيْتُمُ النَّارَ الَّتِي تُورُونَ (71) Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa |
أَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَا أَمْ نَحْنُ الْمُنشِئُونَ (72) Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa |
نَحْنُ جَعَلْنَاهَا تَذْكِرَةً وَمَتَاعًا لِّلْمُقْوِينَ (73) Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji |
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ (74) Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma |
۞ فَلَا أُقْسِمُ بِمَوَاقِعِ النُّجُومِ (75) To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri |
وَإِنَّهُ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌ (76) Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani |
إِنَّهُ لَقُرْآنٌ كَرِيمٌ (77) Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja |
فِي كِتَابٍ مَّكْنُونٍ (78) A cikin wani littafi tsararre |
لَّا يَمَسُّهُ إِلَّا الْمُطَهَّرُونَ (79) Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake |
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ (80) Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta |
أَفَبِهَٰذَا الْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَ (81) Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa |
وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ (82) Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi) |
فَلَوْلَا إِذَا بَلَغَتِ الْحُلْقُومَ (83) To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa) |
وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ (84) Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo |
وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَٰكِن لَّا تُبْصِرُونَ (85) Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani |
فَلَوْلَا إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ (86) To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba |
تَرْجِعُونَهَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (87) Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya |
فَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُقَرَّبِينَ (88) To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta |
فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ (89) Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima |
وَأَمَّا إِن كَانَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ (90) Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma |
فَسَلَامٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ (91) Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma |
وَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُكَذِّبِينَ الضَّالِّينَ (92) Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun |
فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍ (93) Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi |
وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ (94) Da ƙõnuwa da Jahĩm |
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ الْيَقِينِ (95) Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni |
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ (96) Sabõda haka, ka tsarkake* sũnan Ubangijinka, Mai karimci |