×

سورة السجدة باللغة الهوسا

ترجمات القرآنباللغة الهوسا ⬅ سورة السجدة

ترجمة معاني سورة السجدة باللغة الهوسا - Hausa

القرآن باللغة الهوسا - سورة السجدة مترجمة إلى اللغة الهوسا، Surah Sajdah in Hausa. نوفر ترجمة دقيقة سورة السجدة باللغة الهوسا - Hausa, الآيات 30 - رقم السورة 32 - الصفحة 415.

بسم الله الرحمن الرحيم

الم (1)
L̃. M̃
تَنزِيلُ الْكِتَابِ لَا رَيْبَ فِيهِ مِن رَّبِّ الْعَالَمِينَ (2)
Saukar da Littafin bãbu shakka a gare shi, daga Ubangijin tãlikai yake
أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاهُ ۚ بَلْ هُوَ الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوْمًا مَّا أَتَاهُم مِّن نَّذِيرٍ مِّن قَبْلِكَ لَعَلَّهُمْ يَهْتَدُونَ (3)
Kõ sunã cẽwa (Muhammadu ne) ya ƙirƙira shi? Ã'a, shĩ ne gaskiya daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu ba a gabãninka, fãtan zã su shiryu
اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ ۖ مَا لَكُم مِّن دُونِهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا شَفِيعٍ ۚ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ (4)
Allah ne wanda Ya halitta sammai da ƙassai da abin da yake a tsakãninsu a cikin kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba
يُدَبِّرُ الْأَمْرَ مِنَ السَّمَاءِ إِلَى الْأَرْضِ ثُمَّ يَعْرُجُ إِلَيْهِ فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ أَلْفَ سَنَةٍ مِّمَّا تَعُدُّونَ (5)
Yanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan ya tãka zuwa gare Shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shẽkaru dubu ne ga abin da kuke lissafãwa
ذَٰلِكَ عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ (6)
Wannan shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwãyi, Mai jinƙai
الَّذِي أَحْسَنَ كُلَّ شَيْءٍ خَلَقَهُ ۖ وَبَدَأَ خَلْقَ الْإِنسَانِ مِن طِينٍ (7)
Wanda Ya kyautata kõme, Wanda Ya halitta shi. Shi ne kuma Ya fãra halittar mutum daga lãka
ثُمَّ جَعَلَ نَسْلَهُ مِن سُلَالَةٍ مِّن مَّاءٍ مَّهِينٍ (8)
Sa'an nan Ya sanya ɗiyansa daga wani asali na wani ruwa wulãkantacce
ثُمَّ سَوَّاهُ وَنَفَخَ فِيهِ مِن رُّوحِهِ ۖ وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ ۚ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ (9)
Sa'an nan Ya daidaita shi, kuma Ya hũra a cikinsa, daga ruhinSa kuma Ya sanya muku ji, da ganunuwa da zukãta. Gõdiyarku kaɗan ce ƙwarai
وَقَالُوا أَإِذَا ضَلَلْنَا فِي الْأَرْضِ أَإِنَّا لَفِي خَلْقٍ جَدِيدٍ ۚ بَلْ هُم بِلِقَاءِ رَبِّهِمْ كَافِرُونَ (10)
Kuma suka ce: "Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasã, shin, lalle mu, tabbas ne munã zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Ã'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kãfirai
۞ قُلْ يَتَوَفَّاكُم مَّلَكُ الْمَوْتِ الَّذِي وُكِّلَ بِكُمْ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمْ تُرْجَعُونَ (11)
Ka ce: "Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shĩ ne ke karɓar rãyukanku.* Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku
وَلَوْ تَرَىٰ إِذِ الْمُجْرِمُونَ نَاكِسُو رُءُوسِهِمْ عِندَ رَبِّهِمْ رَبَّنَا أَبْصَرْنَا وَسَمِعْنَا فَارْجِعْنَا نَعْمَلْ صَالِحًا إِنَّا مُوقِنُونَ (12)
Kuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne
وَلَوْ شِئْنَا لَآتَيْنَا كُلَّ نَفْسٍ هُدَاهَا وَلَٰكِنْ حَقَّ الْقَوْلُ مِنِّي لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ (13)
Kuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya
فَذُوقُوا بِمَا نَسِيتُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَٰذَا إِنَّا نَسِينَاكُمْ ۖ وَذُوقُوا عَذَابَ الْخُلْدِ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (14)
To, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa
إِنَّمَا يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا الَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُوا بِهَا خَرُّوا سُجَّدًا وَسَبَّحُوا بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ ۩ (15)
Waɗanda ke ĩmãni da ãyõyin Mu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, alhãli kuwa su bã su yin girman kai
تَتَجَافَىٰ جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ (16)
Sãsanninsu nã nĩsanta daga wurãren kwanciya, sunã kiran Ubangijinsu bisa ga tsõro da ɗammãni, kuma sunã ciryawa daga abin da Muka azurta su
فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَّا أُخْفِيَ لَهُم مِّن قُرَّةِ أَعْيُنٍ جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (17)
Sabõda haka wani rai bai san abin da aka ɓõye musu ba, na sanyin idãnu, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa
أَفَمَن كَانَ مُؤْمِنًا كَمَن كَانَ فَاسِقًا ۚ لَّا يَسْتَوُونَ (18)
Shin, wanda ya zama mũmini yanã kamar wanda ya zama fãsiƙi? Bã zã su yi daidai ba
أَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَلَهُمْ جَنَّاتُ الْمَأْوَىٰ نُزُلًا بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (19)
Amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, sunã da gidãjen Aljannar makõma, a kan liyãfa sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa
وَأَمَّا الَّذِينَ فَسَقُوا فَمَأْوَاهُمُ النَّارُ ۖ كُلَّمَا أَرَادُوا أَن يَخْرُجُوا مِنْهَا أُعِيدُوا فِيهَا وَقِيلَ لَهُمْ ذُوقُوا عَذَابَ النَّارِ الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ (20)
Kuma waɗanda suka yi fãsiƙanci to makõmarsu ita ce wuta, kõ da yaushe suka yi nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: "Ku ɗanɗana azãbai wutã, wadda kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita
وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنَ الْعَذَابِ الْأَدْنَىٰ دُونَ الْعَذَابِ الْأَكْبَرِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ (21)
Kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, mafi ƙasƙanci, kãfin a kai ga azãba mafi girma, dõmin fãtan za su kõmo
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِآيَاتِ رَبِّهِ ثُمَّ أَعْرَضَ عَنْهَا ۚ إِنَّا مِنَ الْمُجْرِمِينَ مُنتَقِمُونَ (22)
Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ فَلَا تَكُن فِي مِرْيَةٍ مِّن لِّقَائِهِ ۖ وَجَعَلْنَاهُ هُدًى لِّبَنِي إِسْرَائِيلَ (23)
Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littafi,* sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Banĩ Isrã'ĩla
وَجَعَلْنَا مِنْهُمْ أَئِمَّةً يَهْدُونَ بِأَمْرِنَا لَمَّا صَبَرُوا ۖ وَكَانُوا بِآيَاتِنَا يُوقِنُونَ (24)
Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, sunã shiryarwa da umurnin Mu, a lõkacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance sunã yin yaƙĩni da ãyõyin Mu
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ (25)
Lalle Ubangijinka shĩ ne zai rarrabe a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa
أَوَلَمْ يَهْدِ لَهُمْ كَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَبْلِهِم مِّنَ الْقُرُونِ يَمْشُونَ فِي مَسَاكِنِهِمْ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ ۖ أَفَلَا يَسْمَعُونَ (26)
Shin, ba ya shiryar da su cẽwa da yawa Muka halakara gabãninsu, daga al'ummõmi sunã tafiya a cikin masaukansu?* Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi. Shin, ba su jĩ ne
أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا نَسُوقُ الْمَاءَ إِلَى الْأَرْضِ الْجُرُزِ فَنُخْرِجُ بِهِ زَرْعًا تَأْكُلُ مِنْهُ أَنْعَامُهُمْ وَأَنفُسُهُمْ ۖ أَفَلَا يُبْصِرُونَ (27)
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle Mũ, Munã kõra ruwa zuwa ga ƙasã ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shũka wadda dabbõbinsu, da su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْفَتْحُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (28)
Kuma sunã cẽwa, "Yaushe wannan hukunci yake, aukuwa idan kun kasance mãsu gaskiya
قُلْ يَوْمَ الْفَتْحِ لَا يَنفَعُ الَّذِينَ كَفَرُوا إِيمَانُهُمْ وَلَا هُمْ يُنظَرُونَ (29)
Ka ce: "Ranar hukuncin nan, ĩmãnin waɗanda suka kãfirta bã zai amfãne su ba (a cikinta) kuma bã zã a yi musu jinkiri ba
فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ وَانتَظِرْ إِنَّهُم مُّنتَظِرُونَ (30)
Sabõda haka ka kau da kai daga barinsu, kuma, ka yi jira lalle, sũ ma mãsu jira ne
❮ السورة السابقة السورة التـالية ❯

قراءة المزيد من سور القرآن الكريم :

1- الفاتحة2- البقرة3- آل عمران
4- النساء5- المائدة6- الأنعام
7- الأعراف8- الأنفال9- التوبة
10- يونس11- هود12- يوسف
13- الرعد14- إبراهيم15- الحجر
16- النحل17- الإسراء18- الكهف
19- مريم20- طه21- الأنبياء
22- الحج23- المؤمنون24- النور
25- الفرقان26- الشعراء27- النمل
28- القصص29- العنكبوت30- الروم
31- لقمان32- السجدة33- الأحزاب
34- سبأ35- فاطر36- يس
37- الصافات38- ص39- الزمر
40- غافر41- فصلت42- الشورى
43- الزخرف44- الدخان45- الجاثية
46- الأحقاف47- محمد48- الفتح
49- الحجرات50- ق51- الذاريات
52- الطور53- النجم54- القمر
55- الرحمن56- الواقعة57- الحديد
58- المجادلة59- الحشر60- الممتحنة
61- الصف62- الجمعة63- المنافقون
64- التغابن65- الطلاق66- التحريم
67- الملك68- القلم69- الحاقة
70- المعارج71- نوح72- الجن
73- المزمل74- المدثر75- القيامة
76- الإنسان77- المرسلات78- النبأ
79- النازعات80- عبس81- التكوير
82- الإنفطار83- المطففين84- الانشقاق
85- البروج86- الطارق87- الأعلى
88- الغاشية89- الفجر90- البلد
91- الشمس92- الليل93- الضحى
94- الشرح95- التين96- العلق
97- القدر98- البينة99- الزلزلة
100- العاديات101- القارعة102- التكاثر
103- العصر104- الهمزة105- الفيل
106- قريش107- الماعون108- الكوثر
109- الكافرون110- النصر111- المسد
112- الإخلاص113- الفلق114- الناس