إِذَا السَّمَاءُ انفَطَرَتْ (1) Idan sama ta tsãge |
وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انتَثَرَتْ (2) Kuma idan taurãri suka wãtse |
وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ (3) Kuma idan tẽkuna aka facce su |
وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ (4) Kuma idan kaburbura aka tõne su |
عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ (5) Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar |
يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ (6) Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci |
الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ (7) Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka |
فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاءَ رَكَّبَكَ (8) A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta |
كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ (9) A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako |
وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ (10) Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara |
كِرَامًا كَاتِبِينَ (11) Mãsu daraja, marubũta |
يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ (12) Sunã sanin abin da kuke aikatãwa |
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ (13) Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima |
وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ (14) Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm |
يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ (15) Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako |
وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ (16) Bã zã su faku daga gare ta ba |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ (17) Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako |
ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ (18) Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako |
يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْئًا ۖ وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ (19) Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake |