عَبَسَ وَتَوَلَّىٰ (1) Yã game huska* kuma ya jũya bãya |
أَن جَاءَهُ الْأَعْمَىٰ (2) Sabõda makãho yã je masa |
وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّىٰ (3) To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka |
أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ الذِّكْرَىٰ (4) Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi |
أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَىٰ (5) Amma wanda ya wadãtu da dũkiya |
فَأَنتَ لَهُ تَصَدَّىٰ (6) Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi |
وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ (7) To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba |
وَأَمَّا مَن جَاءَكَ يَسْعَىٰ (8) Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa |
وَهُوَ يَخْشَىٰ (9) Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah |
فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّىٰ (10) Kai kuma kã shagala ga barinsa |
كَلَّا إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ (11) A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce |
فَمَن شَاءَ ذَكَرَهُ (12) Sabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah) |
فِي صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ (13) (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa |
مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍ (14) Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa |
بِأَيْدِي سَفَرَةٍ (15) A cikin hannãyen mala'iku marubũta |
كِرَامٍ بَرَرَةٍ (16) Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah |
قُتِلَ الْإِنسَانُ مَا أَكْفَرَهُ (17) An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa |
مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ (18) Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi |
مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُ فَقَدَّرَهُ (19) Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye) |
ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ (20) Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa |
ثُمَّ أَمَاتَهُ فَأَقْبَرَهُ (21) Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari |
ثُمَّ إِذَا شَاءَ أَنشَرَهُ (22) Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi |
كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ (23) Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari) |
فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ إِلَىٰ طَعَامِهِ (24) To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa |
أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاءَ صَبًّا (25) Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa |
ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا (26) Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa |
فَأَنبَتْنَا فِيهَا حَبًّا (27) Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta |
وَعِنَبًا وَقَضْبًا (28) Da inabi da ciyãwa |
وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا (29) Da zaitũni da itãcen dabĩno |
وَحَدَائِقَ غُلْبًا (30) Da lambuna, mãsu yawan itãce |
وَفَاكِهَةً وَأَبًّا (31) Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi |
مَّتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ (32) Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku |
فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ (33) To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo |
يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ (34) Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa |
وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ (35) Da uwarsa da ubansa |
وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ (36) Da mãtarsa da ɗiyansa |
لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ (37) Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi |
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ (38) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne |
ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ (39) Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra |
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ (40) Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu |
تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ (41) Baƙi zai rufe su |
أُولَٰئِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ (42) Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu) |