×

سورة الجاثية باللغة الهوسا

ترجمات القرآنباللغة الهوسا ⬅ سورة الجاثية

ترجمة معاني سورة الجاثية باللغة الهوسا - Hausa

القرآن باللغة الهوسا - سورة الجاثية مترجمة إلى اللغة الهوسا، Surah Jathiyah in Hausa. نوفر ترجمة دقيقة سورة الجاثية باللغة الهوسا - Hausa, الآيات 37 - رقم السورة 45 - الصفحة 499.

بسم الله الرحمن الرحيم

حم (1)
Ḥ. M̃
تَنزِيلُ الْكِتَابِ مِنَ اللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ (2)
Saukar Littãfi daga Allah Mabuwãyi Mai hikima yake
إِنَّ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَآيَاتٍ لِّلْمُؤْمِنِينَ (3)
Lalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi* ga mãsu ĩmãni
وَفِي خَلْقِكُمْ وَمَا يَبُثُّ مِن دَابَّةٍ آيَاتٌ لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ (4)
Kuma a cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yaƙĩni
وَاخْتِلَافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَمَا أَنزَلَ اللَّهُ مِنَ السَّمَاءِ مِن رِّزْقٍ فَأَحْيَا بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَتَصْرِيفِ الرِّيَاحِ آيَاتٌ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ (5)
Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali
تِلْكَ آيَاتُ اللَّهِ نَتْلُوهَا عَلَيْكَ بِالْحَقِّ ۖ فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَ اللَّهِ وَآيَاتِهِ يُؤْمِنُونَ (6)
Waɗancan ãyõyin Allah ne, Munã karanta su gare ka da gaskiya. To, da wane lãbãri bãyan Allah da ãyõyinSa suke yin ĩmãni
وَيْلٌ لِّكُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ (7)
Bone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi
يَسْمَعُ آيَاتِ اللَّهِ تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ثُمَّ يُصِرُّ مُسْتَكْبِرًا كَأَن لَّمْ يَسْمَعْهَا ۖ فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ (8)
Yanã jin ãyõyin Allah anã karanta su a kansa, sa'an nan ya dõge yanã makãngari, kamar bai jĩ su ba. To, ka yi masa bushara da azãba mai raɗaɗi
وَإِذَا عَلِمَ مِنْ آيَاتِنَا شَيْئًا اتَّخَذَهَا هُزُوًا ۚ أُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مُّهِينٌ (9)
Kuma har idan ya san wani abu daga ãyõyin Mu, sai ya rika su da izgili. Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa (a dũniya)
مِّن وَرَائِهِمْ جَهَنَّمُ ۖ وَلَا يُغْنِي عَنْهُم مَّا كَسَبُوا شَيْئًا وَلَا مَا اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ أَوْلِيَاءَ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ (10)
Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma
هَٰذَا هُدًى ۖ وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ رَبِّهِمْ لَهُمْ عَذَابٌ مِّن رِّجْزٍ أَلِيمٌ (11)
Wannan (Alƙur'ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi
۞ اللَّهُ الَّذِي سَخَّرَ لَكُمُ الْبَحْرَ لِتَجْرِيَ الْفُلْكُ فِيهِ بِأَمْرِهِ وَلِتَبْتَغُوا مِن فَضْلِهِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ (12)
Allah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalar Sa, kuma tsammãninku zã ku gõde
وَسَخَّرَ لَكُم مَّا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا مِّنْهُ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ (13)
Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni
قُل لِّلَّذِينَ آمَنُوا يَغْفِرُوا لِلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ أَيَّامَ اللَّهِ لِيَجْزِيَ قَوْمًا بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ (14)
Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, *dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa
مَنْ عَمِلَ صَالِحًا فَلِنَفْسِهِ ۖ وَمَنْ أَسَاءَ فَعَلَيْهَا ۖ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمْ تُرْجَعُونَ (15)
Wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a kansa. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku
وَلَقَدْ آتَيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ وَرَزَقْنَاهُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ (16)
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai* (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu)
وَآتَيْنَاهُم بَيِّنَاتٍ مِّنَ الْأَمْرِ ۖ فَمَا اخْتَلَفُوا إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ (17)
Kuma Muka bã su hujjõji na umarni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna)
ثُمَّ جَعَلْنَاكَ عَلَىٰ شَرِيعَةٍ مِّنَ الْأَمْرِ فَاتَّبِعْهَا وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَ الَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ (18)
Sa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin. Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba
إِنَّهُمْ لَن يُغْنُوا عَنكَ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا ۚ وَإِنَّ الظَّالِمِينَ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۖ وَاللَّهُ وَلِيُّ الْمُتَّقِينَ (19)
Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa
هَٰذَا بَصَائِرُ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ (20)
wannan (Alkur'ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni
أَمْ حَسِبَ الَّذِينَ اجْتَرَحُوا السَّيِّئَاتِ أَن نَّجْعَلَهُمْ كَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَوَاءً مَّحْيَاهُمْ وَمَمَاتُهُمْ ۚ سَاءَ مَا يَحْكُمُونَ (21)
Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã
وَخَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ وَلِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍ بِمَا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ (22)
Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba
أَفَرَأَيْتَ مَنِ اتَّخَذَ إِلَٰهَهُ هَوَاهُ وَأَضَلَّهُ اللَّهُ عَلَىٰ عِلْمٍ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمْعِهِ وَقَلْبِهِ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِ غِشَاوَةً فَمَن يَهْدِيهِ مِن بَعْدِ اللَّهِ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ (23)
Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi,* Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba
وَقَالُوا مَا هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا يُهْلِكُنَا إِلَّا الدَّهْرُ ۚ وَمَا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلَّا يَظُنُّونَ (24)
Kuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa (da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ مَّا كَانَ حُجَّتَهُمْ إِلَّا أَن قَالُوا ائْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (25)
Kuma idan anã karanta ãyõyin Mu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya
قُلِ اللَّهُ يُحْيِيكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يَجْمَعُكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ لَا رَيْبَ فِيهِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ (26)
Ka ce: "Allah ne ke rãyar* da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba
وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَخْسَرُ الْمُبْطِلُونَ (27)
Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra
وَتَرَىٰ كُلَّ أُمَّةٍ جَاثِيَةً ۚ كُلُّ أُمَّةٍ تُدْعَىٰ إِلَىٰ كِتَابِهَا الْيَوْمَ تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (28)
Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. (A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa
هَٰذَا كِتَابُنَا يَنطِقُ عَلَيْكُم بِالْحَقِّ ۚ إِنَّا كُنَّا نَسْتَنسِخُ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (29)
Wannan littãfin Mu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun kasance Muna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa
فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَيُدْخِلُهُمْ رَبُّهُمْ فِي رَحْمَتِهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْمُبِينُ (30)
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne
وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا أَفَلَمْ تَكُنْ آيَاتِي تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَاسْتَكْبَرْتُمْ وَكُنتُمْ قَوْمًا مُّجْرِمِينَ (31)
Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩ Nã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi
وَإِذَا قِيلَ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ وَالسَّاعَةُ لَا رَيْبَ فِيهَا قُلْتُم مَّا نَدْرِي مَا السَّاعَةُ إِن نَّظُنُّ إِلَّا ظَنًّا وَمَا نَحْنُ بِمُسْتَيْقِنِينَ (32)
Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba
وَبَدَا لَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا عَمِلُوا وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ (33)
Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu
وَقِيلَ الْيَوْمَ نَنسَاكُمْ كَمَا نَسِيتُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَٰذَا وَمَأْوَاكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّاصِرِينَ (34)
Kuma aka ce: "A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako
ذَٰلِكُم بِأَنَّكُمُ اتَّخَذْتُمْ آيَاتِ اللَّهِ هُزُوًا وَغَرَّتْكُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا ۚ فَالْيَوْمَ لَا يُخْرَجُونَ مِنْهَا وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ (35)
Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba
فَلِلَّهِ الْحَمْدُ رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَرَبِّ الْأَرْضِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (36)
Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu
وَلَهُ الْكِبْرِيَاءُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (37)
Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima
❮ السورة السابقة السورة التـالية ❯

قراءة المزيد من سور القرآن الكريم :

1- الفاتحة2- البقرة3- آل عمران
4- النساء5- المائدة6- الأنعام
7- الأعراف8- الأنفال9- التوبة
10- يونس11- هود12- يوسف
13- الرعد14- إبراهيم15- الحجر
16- النحل17- الإسراء18- الكهف
19- مريم20- طه21- الأنبياء
22- الحج23- المؤمنون24- النور
25- الفرقان26- الشعراء27- النمل
28- القصص29- العنكبوت30- الروم
31- لقمان32- السجدة33- الأحزاب
34- سبأ35- فاطر36- يس
37- الصافات38- ص39- الزمر
40- غافر41- فصلت42- الشورى
43- الزخرف44- الدخان45- الجاثية
46- الأحقاف47- محمد48- الفتح
49- الحجرات50- ق51- الذاريات
52- الطور53- النجم54- القمر
55- الرحمن56- الواقعة57- الحديد
58- المجادلة59- الحشر60- الممتحنة
61- الصف62- الجمعة63- المنافقون
64- التغابن65- الطلاق66- التحريم
67- الملك68- القلم69- الحاقة
70- المعارج71- نوح72- الجن
73- المزمل74- المدثر75- القيامة
76- الإنسان77- المرسلات78- النبأ
79- النازعات80- عبس81- التكوير
82- الإنفطار83- المطففين84- الانشقاق
85- البروج86- الطارق87- الأعلى
88- الغاشية89- الفجر90- البلد
91- الشمس92- الليل93- الضحى
94- الشرح95- التين96- العلق
97- القدر98- البينة99- الزلزلة
100- العاديات101- القارعة102- التكاثر
103- العصر104- الهمزة105- الفيل
106- قريش107- الماعون108- الكوثر
109- الكافرون110- النصر111- المسد
112- الإخلاص113- الفلق114- الناس