إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ (1) Idan rãna aka shafe haskenta |
وَإِذَا النُّجُومُ انكَدَرَتْ (2) Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani) |
وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ (3) Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su |
وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ (4) Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba |
وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ (5) Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su |
وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ (6) Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta |
وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ (7) Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu |
وَإِذَا الْمَوْءُودَةُ سُئِلَتْ (8) Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta |
بِأَيِّ ذَنبٍ قُتِلَتْ (9) Sabõda wane laifi ne aka kashe ta |
وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ (10) Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su) |
وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ (11) Kuma idan sama aka fẽɗe ta |
وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ (12) Kuma idan Jahĩm aka hũra ta |
وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ (13) Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita |
عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا أَحْضَرَتْ (14) Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan) |
فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ (15) To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba |
الْجَوَارِ الْكُنَّسِ (16) Mãsu gudu suna ɓũya |
وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ (17) Da dare idan ya bãyar da bãya |
وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ (18) Da sãfiya idan ta yi lumfashi |
إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ (19) Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah |
ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ (20) Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi |
مُّطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ (21) Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce |
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ (22) Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne |
وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ (23) Kuma lalle ne, yã gan shi* a cikin sararin sama mabayyani |
وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ (24) Kuma shi, ga gaibi* bã mai rowa ba ne |
وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَّجِيمٍ (25) Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce |
فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ (26) Shin, a inã zã ku tafi |
إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ (27) Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai |
لِمَن شَاءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ (28) Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu |
وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ (29) Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda |