الْحَاقَّةُ (1) Kiran gaskiya |
مَا الْحَاقَّةُ (2) Mẽne ne kiran gaskiya |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحَاقَّةُ (3) Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya |
كَذَّبَتْ ثَمُودُ وَعَادٌ بِالْقَارِعَةِ (4) Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya |
فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهْلِكُوا بِالطَّاغِيَةِ (5) To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani |
وَأَمَّا عَادٌ فَأُهْلِكُوا بِرِيحٍ صَرْصَرٍ عَاتِيَةٍ (6) Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi |
سَخَّرَهَا عَلَيْهِمْ سَبْعَ لَيَالٍ وَثَمَانِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومًا فَتَرَى الْقَوْمَ فِيهَا صَرْعَىٰ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ خَاوِيَةٍ (7) (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi |
فَهَلْ تَرَىٰ لَهُم مِّن بَاقِيَةٍ (8) To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu |
وَجَاءَ فِرْعَوْنُ وَمَن قَبْلَهُ وَالْمُؤْتَفِكَاتُ بِالْخَاطِئَةِ (9) Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi |
فَعَصَوْا رَسُولَ رَبِّهِمْ فَأَخَذَهُمْ أَخْذَةً رَّابِيَةً (10) Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani) |
إِنَّا لَمَّا طَغَى الْمَاءُ حَمَلْنَاكُمْ فِي الْجَارِيَةِ (11) Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan |
لِنَجْعَلَهَا لَكُمْ تَذْكِرَةً وَتَعِيَهَا أُذُنٌ وَاعِيَةٌ (12) Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi) |
فَإِذَا نُفِخَ فِي الصُّورِ نَفْخَةٌ وَاحِدَةٌ (13) To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya |
وَحُمِلَتِ الْأَرْضُ وَالْجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةً وَاحِدَةً (14) Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya |
فَيَوْمَئِذٍ وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ (15) A ran nan, mai aukuwa zã ta auku |
وَانشَقَّتِ السَّمَاءُ فَهِيَ يَوْمَئِذٍ وَاهِيَةٌ (16) Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce |
وَالْمَلَكُ عَلَىٰ أَرْجَائِهَا ۚ وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ يَوْمَئِذٍ ثَمَانِيَةٌ (17) Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar |
يَوْمَئِذٍ تُعْرَضُونَ لَا تَخْفَىٰ مِنكُمْ خَافِيَةٌ (18) A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa |
فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ فَيَقُولُ هَاؤُمُ اقْرَءُوا كِتَابِيَهْ (19) To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina |
إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلَاقٍ حِسَابِيَهْ (20) Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne |
فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ (21) Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda |
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ (22) A cikin Aljanna maɗaukakiya |
قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ (23) Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba) |
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا أَسْلَفْتُمْ فِي الْأَيَّامِ الْخَالِيَةِ (24) (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige |
وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِشِمَالِهِ فَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُوتَ كِتَابِيَهْ (25) Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba |
وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيَهْ (26) Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba |
يَا لَيْتَهَا كَانَتِ الْقَاضِيَةَ (27) In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce |
مَا أَغْنَىٰ عَنِّي مَالِيَهْ ۜ (28) Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba |
هَلَكَ عَنِّي سُلْطَانِيَهْ (29) Ĩkona ya ɓace mini |
خُذُوهُ فَغُلُّوهُ (30) (Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi |
ثُمَّ الْجَحِيمَ صَلُّوهُ (31) Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi |
ثُمَّ فِي سِلْسِلَةٍ ذَرْعُهَا سَبْعُونَ ذِرَاعًا فَاسْلُكُوهُ (32) Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi |
إِنَّهُ كَانَ لَا يُؤْمِنُ بِاللَّهِ الْعَظِيمِ (33) Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma |
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ الْمِسْكِينِ (34) Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci |
فَلَيْسَ لَهُ الْيَوْمَ هَاهُنَا حَمِيمٌ (35) Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi |
وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنْ غِسْلِينٍ (36) Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn |
لَّا يَأْكُلُهُ إِلَّا الْخَاطِئُونَ (37) Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci |
فَلَا أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ (38) To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba |
وَمَا لَا تُبْصِرُونَ (39) Da abin da bã ku iya gani |
إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ (40) Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne |
وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِرٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تُؤْمِنُونَ (41) Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata |
وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ (42) Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa |
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ (43) Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka |
وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الْأَقَاوِيلِ (44) Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu |
لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ (45) Dã Mun kãma shi da dãma |
ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ (46) sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã |
فَمَا مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ (47) Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbar Mu) daga gare shi |
وَإِنَّهُ لَتَذْكِرَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ (48) Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa |
وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ (49) Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa |
وَإِنَّهُ لَحَسْرَةٌ عَلَى الْكَافِرِينَ (50) Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai |
وَإِنَّهُ لَحَقُّ الْيَقِينِ (51) Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙini |
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ (52) Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma |