وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ (1) Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa |
الَّذِينَ إِذَا اكْتَالُوا عَلَى النَّاسِ يَسْتَوْفُونَ (2) Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu |
وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ (3) Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa |
أَلَا يَظُنُّ أُولَٰئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ (4) Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba |
لِيَوْمٍ عَظِيمٍ (5) Domin yini mai girma |
يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ (6) Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta |
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍ (7) Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا سِجِّينٌ (8) Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn |
كِتَابٌ مَّرْقُومٌ (9) Wani ittãfi ne rubũtacce |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (10) Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa |
الَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ (11) Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako |
وَمَا يُكَذِّبُ بِهِ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ (12) Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi |
إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ (13) Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne |
كَلَّا ۖ بَلْ ۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ (14) A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu |
كَلَّا إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ (15) A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne |
ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُو الْجَحِيمِ (16) Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne |
ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ (17) Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi |
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْأَبْرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ (18) A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا عِلِّيُّونَ (19) Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna |
كِتَابٌ مَّرْقُومٌ (20) Wani littãfi ne rubũtacce |
يَشْهَدُهُ الْمُقَرَّبُونَ (21) Muƙarrabai* suke halarta shi |
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ (22) Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima |
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ (23) A kan karagu, suna ta kallo |
تَعْرِفُ فِي وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ النَّعِيمِ (24) Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima |
يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ (25) Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta |
خِتَامُهُ مِسْكٌ ۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ الْمُتَنَافِسُونَ (26) ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma |
وَمِزَاجُهُ مِن تَسْنِيمٍ (27) Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake |
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا الْمُقَرَّبُونَ (28) (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi |
إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُوا مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا يَضْحَكُونَ (29) Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya |
وَإِذَا مَرُّوا بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ (30) Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe |
وَإِذَا انقَلَبُوا إِلَىٰ أَهْلِهِمُ انقَلَبُوا فَكِهِينَ (31) Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci |
وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَضَالُّونَ (32) Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne |
وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَ (33) Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu |
فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آمَنُوا مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ (34) To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya |
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ (35) A kan karagu, suna ta kallo |
هَلْ ثُوِّبَ الْكُفَّارُ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ (36) Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa |