وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰ (1) Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa |
وَالنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ (2) Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa |
وَمَا خَلَقَ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ (3) Da abin da ya halitta namiji da mace |
إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّىٰ (4) Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke |
فَأَمَّا مَنْ أَعْطَىٰ وَاتَّقَىٰ (5) To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa |
وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَىٰ (6) Kuma ya gaskata kalma* mai kyãwo |
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَىٰ (7) To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi |
وَأَمَّا مَن بَخِلَ وَاسْتَغْنَىٰ (8) Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa |
وَكَذَّبَ بِالْحُسْنَىٰ (9) Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo |
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْعُسْرَىٰ (10) To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani |
وَمَا يُغْنِي عَنْهُ مَالُهُ إِذَا تَرَدَّىٰ (11) Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta) |
إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَىٰ (12) Lãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya |
وَإِنَّ لَنَا لَلْآخِرَةَ وَالْأُولَىٰ (13) Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne |
فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّىٰ (14) Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka |
لَا يَصْلَاهَا إِلَّا الْأَشْقَى (15) Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa |
الَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ (16) Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya |
وَسَيُجَنَّبُهَا الْأَتْقَى (17) Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta |
الَّذِي يُؤْتِي مَالَهُ يَتَزَكَّىٰ (18) Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka |
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَىٰ (19) Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta |
إِلَّا ابْتِغَاءَ وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَىٰ (20) Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka |
وَلَسَوْفَ يَرْضَىٰ (21) To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi) |