وَالصَّافَّاتِ صَفًّا (1) Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi) |
فَالزَّاجِرَاتِ زَجْرًا (2) Sa'an nan mãsu yin tsãwa* dõmin gargaɗi |
فَالتَّالِيَاتِ ذِكْرًا (3) Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa |
إِنَّ إِلَٰهَكُمْ لَوَاحِدٌ (4) Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne |
رَّبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ الْمَشَارِقِ (5) Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã |
إِنَّا زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِزِينَةٍ الْكَوَاكِبِ (6) Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri |
وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَانٍ مَّارِدٍ (7) Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai |
لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى الْمَلَإِ الْأَعْلَىٰ وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍ (8) Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe |
دُحُورًا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌ (9) Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya |
إِلَّا مَنْ خَطِفَ الْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُ شِهَابٌ ثَاقِبٌ (10) Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi |
فَاسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَم مَّنْ خَلَقْنَا ۚ إِنَّا خَلَقْنَاهُم مِّن طِينٍ لَّازِبٍ (11) Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri |
بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَ (12) Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili |
وَإِذَا ذُكِّرُوا لَا يَذْكُرُونَ (13) Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa |
وَإِذَا رَأَوْا آيَةً يَسْتَسْخِرُونَ (14) Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili |
وَقَالُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ (15) Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne |
أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ (16) Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne |
أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ (17) Ashe kõ da ubanninmu na farko |
قُلْ نَعَمْ وَأَنتُمْ دَاخِرُونَ (18) Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu |
فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَ (19) Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi |
وَقَالُوا يَا وَيْلَنَا هَٰذَا يَوْمُ الدِّينِ (20) Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako |
هَٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ (21) Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa |
۞ احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأَزْوَاجَهُمْ وَمَا كَانُوا يَعْبُدُونَ (22) Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa |
مِن دُونِ اللَّهِ فَاهْدُوهُمْ إِلَىٰ صِرَاطِ الْجَحِيمِ (23) Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm |
وَقِفُوهُمْ ۖ إِنَّهُم مَّسْئُولُونَ (24) Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne |
مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَ (25) Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna |
بَلْ هُمُ الْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَ (26) Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne |
وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ (27) Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna |
قَالُوا إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ الْيَمِينِ (28) Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince) |
قَالُوا بَل لَّمْ تَكُونُوا مُؤْمِنِينَ (29) Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba |
وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَانٍ ۖ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَاغِينَ (30) Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka |
فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَا ۖ إِنَّا لَذَائِقُونَ (31) Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne |
فَأَغْوَيْنَاكُمْ إِنَّا كُنَّا غَاوِينَ (32) Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu |
فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ (33) To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ (34) Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi |
إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ (35) Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai |
وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُو آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍ (36) Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci |
بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَ (37) Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni |
إِنَّكُمْ لَذَائِقُو الْعَذَابِ الْأَلِيمِ (38) Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne |
وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (39) Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa |
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ (40) Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake |
أُولَٰئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌ (41) Waɗannan sunã da abinci sananne |
فَوَاكِهُ ۖ وَهُم مُّكْرَمُونَ (42) Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa |
فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ (43) A cikin gidãjen Aljannar ni'ima |
عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَ (44) A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna |
يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ (45) Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari |
بَيْضَاءَ لَذَّةٍ لِّلشَّارِبِينَ (46) Farã mai dãɗi ga mashãyan |
لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَ (47) A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba |
وَعِندَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ عِينٌ (48) Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu |
كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌ (49) Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye |
فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ (50) Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna |
قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٌ (51) Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya) |
يَقُولُ أَإِنَّكَ لَمِنَ الْمُصَدِّقِينَ (52) Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne |
أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَدِينُونَ (53) Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne |
قَالَ هَلْ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ (54) (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi) |
فَاطَّلَعَ فَرَآهُ فِي سَوَاءِ الْجَحِيمِ (55) Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim |
قَالَ تَاللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرْدِينِ (56) Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni |
وَلَوْلَا نِعْمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ الْمُحْضَرِينَ (57) Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã) |
أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ (58) Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba |
إِلَّا مَوْتَتَنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ (59) Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba |
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (60) Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma |
لِمِثْلِ هَٰذَا فَلْيَعْمَلِ الْعَامِلُونَ (61) Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa |
أَذَٰلِكَ خَيْرٌ نُّزُلًا أَمْ شَجَرَةُ الزَّقُّومِ (62) Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm |
إِنَّا جَعَلْنَاهَا فِتْنَةً لِّلظَّالِمِينَ (63) Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai |
إِنَّهَا شَجَرَةٌ تَخْرُجُ فِي أَصْلِ الْجَحِيمِ (64) Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm |
طَلْعُهَا كَأَنَّهُ رُءُوسُ الشَّيَاطِينِ (65) Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne |
فَإِنَّهُمْ لَآكِلُونَ مِنْهَا فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ (66) To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta |
ثُمَّ إِنَّ لَهُمْ عَلَيْهَا لَشَوْبًا مِّنْ حَمِيمٍ (67) Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi |
ثُمَّ إِنَّ مَرْجِعَهُمْ لَإِلَى الْجَحِيمِ (68) Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take |
إِنَّهُمْ أَلْفَوْا آبَاءَهُمْ ضَالِّينَ (69) Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu |
فَهُمْ عَلَىٰ آثَارِهِمْ يُهْرَعُونَ (70) Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa |
وَلَقَدْ ضَلَّ قَبْلَهُمْ أَكْثَرُ الْأَوَّلِينَ (71) Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu |
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ (72) Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu |
فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُنذَرِينَ (73) Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance |
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ (74) Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake |
وَلَقَدْ نَادَانَا نُوحٌ فَلَنِعْمَ الْمُجِيبُونَ (75) Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu |
وَنَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ (76) Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba |
وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَهُ هُمُ الْبَاقِينَ (77) Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa |
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ (78) Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe |
سَلَامٌ عَلَىٰ نُوحٍ فِي الْعَالَمِينَ (79) Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ (80) Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa |
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ (81) Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai |
ثُمَّ أَغْرَقْنَا الْآخَرِينَ (82) Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu |
۞ وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِ لَإِبْرَاهِيمَ (83) Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake |
إِذْ جَاءَ رَبَّهُ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ (84) A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya |
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَاذَا تَعْبُدُونَ (85) A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa |
أَئِفْكًا آلِهَةً دُونَ اللَّهِ تُرِيدُونَ (86) Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa |
فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ الْعَالَمِينَ (87) To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu |
فَنَظَرَ نَظْرَةً فِي النُّجُومِ (88) Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri |
فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٌ (89) Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne |
فَتَوَلَّوْا عَنْهُ مُدْبِرِينَ (90) Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya |
فَرَاغَ إِلَىٰ آلِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ (91) Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba |
مَا لَكُمْ لَا تَنطِقُونَ (92) Me ya sãme ku, bã ku magana |
فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبًا بِالْيَمِينِ (93) Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma |
فَأَقْبَلُوا إِلَيْهِ يَزِفُّونَ (94) Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa |
قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ (95) Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa |
وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ (96) Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa |
قَالُوا ابْنُوا لَهُ بُنْيَانًا فَأَلْقُوهُ فِي الْجَحِيمِ (97) Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm |
فَأَرَادُوا بِهِ كَيْدًا فَجَعَلْنَاهُمُ الْأَسْفَلِينَ (98) Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci |
وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهْدِينِ (99) Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni |
رَبِّ هَبْ لِي مِنَ الصَّالِحِينَ (100) Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne |
فَبَشَّرْنَاهُ بِغُلَامٍ حَلِيمٍ (101) Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro *mai haƙuri |
فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ السَّعْيَ قَالَ يَا بُنَيَّ إِنِّي أَرَىٰ فِي الْمَنَامِ أَنِّي أَذْبَحُكَ فَانظُرْ مَاذَا تَرَىٰ ۚ قَالَ يَا أَبَتِ افْعَلْ مَا تُؤْمَرُ ۖ سَتَجِدُنِي إِن شَاءَ اللَّهُ مِنَ الصَّابِرِينَ (102) To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri |
فَلَمَّا أَسْلَمَا وَتَلَّهُ لِلْجَبِينِ (103) Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago |
وَنَادَيْنَاهُ أَن يَا إِبْرَاهِيمُ (104) Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm |
قَدْ صَدَّقْتَ الرُّؤْيَا ۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ (105) Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa |
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ الْبَلَاءُ الْمُبِينُ (106) Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna |
وَفَدَيْنَاهُ بِذِبْحٍ عَظِيمٍ (107) Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma |
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ (108) Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe |
سَلَامٌ عَلَىٰ إِبْرَاهِيمَ (109) Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm |
كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ (110) Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa |
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ (111) Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai |
وَبَشَّرْنَاهُ بِإِسْحَاقَ نَبِيًّا مِّنَ الصَّالِحِينَ (112) Kuma Muka yi masa bushãra* Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne |
وَبَارَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَىٰ إِسْحَاقَ ۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحْسِنٌ وَظَالِمٌ لِّنَفْسِهِ مُبِينٌ (113) Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin) |
وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَارُونَ (114) Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna |
وَنَجَّيْنَاهُمَا وَقَوْمَهُمَا مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ (115) Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma |
وَنَصَرْنَاهُمْ فَكَانُوا هُمُ الْغَالِبِينَ (116) Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya |
وَآتَيْنَاهُمَا الْكِتَابَ الْمُسْتَبِينَ (117) Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni |
وَهَدَيْنَاهُمَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ (118) Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya |
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِمَا فِي الْآخِرِينَ (119) Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe |
سَلَامٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَارُونَ (120) Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ (121) Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa |
إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ (122) Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai |
وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ (123) Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni |
إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَلَا تَتَّقُونَ (124) A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba |
أَتَدْعُونَ بَعْلًا وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ الْخَالِقِينَ (125) Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta |
اللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ (126) Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko |
فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ (127) Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã) |
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ (128) Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake |
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ (129) Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe |
سَلَامٌ عَلَىٰ إِلْ يَاسِينَ (130) Aminci ya tabbata ga Ilyãs |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ (131) Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa |
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ (132) Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai |
وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ الْمُرْسَلِينَ (133) Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni |
إِذْ نَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ أَجْمَعِينَ (134) A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya |
إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَ (135) Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba) |
ثُمَّ دَمَّرْنَا الْآخَرِينَ (136) Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen |
وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِم مُّصْبِحِينَ (137) Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci |
وَبِاللَّيْلِ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ (138) Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba |
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ (139) Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni |
إِذْ أَبَقَ إِلَى الْفُلْكِ الْمَشْحُونِ (140) A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi |
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ الْمُدْحَضِينَ (141) Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya |
فَالْتَقَمَهُ الْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌ (142) Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi |
فَلَوْلَا أَنَّهُ كَانَ مِنَ الْمُسَبِّحِينَ (143) To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba |
لَلَبِثَ فِي بَطْنِهِ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ (144) Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su |
۞ فَنَبَذْنَاهُ بِالْعَرَاءِ وَهُوَ سَقِيمٌ (145) Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya |
وَأَنبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةً مِّن يَقْطِينٍ (146) Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi |
وَأَرْسَلْنَاهُ إِلَىٰ مِائَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَ (147) Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka) |
فَآمَنُوا فَمَتَّعْنَاهُمْ إِلَىٰ حِينٍ (148) Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci |
فَاسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ الْبَنَاتُ وَلَهُمُ الْبَنُونَ (149) Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza |
أَمْ خَلَقْنَا الْمَلَائِكَةَ إِنَاثًا وَهُمْ شَاهِدُونَ (150) Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce |
أَلَا إِنَّهُم مِّنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَ (151) To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa |
وَلَدَ اللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ (152) Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne |
أَصْطَفَى الْبَنَاتِ عَلَى الْبَنِينَ (153) Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza |
مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ (154) Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci) |
أَفَلَا تَذَكَّرُونَ (155) Shin, bã ku tunãni |
أَمْ لَكُمْ سُلْطَانٌ مُّبِينٌ (156) Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne |
فَأْتُوا بِكِتَابِكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (157) To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya |
وَجَعَلُوا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجِنَّةِ نَسَبًا ۚ وَلَقَدْ عَلِمَتِ الْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ (158) Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã) |
سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ (159) Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa |
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ (160) Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake |
فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ (161) To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa |
مَا أَنتُمْ عَلَيْهِ بِفَاتِنِينَ (162) Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi |
إِلَّا مَنْ هُوَ صَالِ الْجَحِيمِ (163) Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm |
وَمَا مِنَّا إِلَّا لَهُ مَقَامٌ مَّعْلُومٌ (164) Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,* fãce yanã da matsayi sananne |
وَإِنَّا لَنَحْنُ الصَّافُّونَ (165) Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda) |
وَإِنَّا لَنَحْنُ الْمُسَبِّحُونَ (166) Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi |
وَإِن كَانُوا لَيَقُولُونَ (167) Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa |
لَوْ أَنَّ عِندَنَا ذِكْرًا مِّنَ الْأَوَّلِينَ (168) Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko |
لَكُنَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ (169) Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake |
فَكَفَرُوا بِهِ ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ (170) Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani |
وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا الْمُرْسَلِينَ (171) Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni |
إِنَّهُمْ لَهُمُ الْمَنصُورُونَ (172) Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako |
وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ الْغَالِبُونَ (173) Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya |
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ (174) Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci |
وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ (175) Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani |
أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ (176) Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa |
فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَاءَ صَبَاحُ الْمُنذَرِينَ (177) To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana |
وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ (178) Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci |
وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ (179) Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa |
سُبْحَانَ رَبِّكَ رَبِّ الْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ (180) Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa |
وَسَلَامٌ عَلَى الْمُرْسَلِينَ (181) Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni |
وَالْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (182) Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu |