لَا أُقْسِمُ بِيَوْمِ الْقِيَامَةِ (1) Bã sai Nã yi rantsuwa* da Rãnar ¡iyãma ba |
وَلَا أُقْسِمُ بِالنَّفْسِ اللَّوَّامَةِ (2) Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin* kansa ba |
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُ (3) Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba |
بَلَىٰ قَادِرِينَ عَلَىٰ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُ (4) Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa |
بَلْ يُرِيدُ الْإِنسَانُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُ (5) Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa |
يَسْأَلُ أَيَّانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ (6) Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma |
فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ (7) To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli) |
وَخَسَفَ الْقَمَرُ (8) Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe) |
وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ (9) Aka tãra rãnã da watã |
يَقُولُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ (10) Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu |
كَلَّا لَا وَزَرَ (11) A'aha! bãbu mafaka |
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمُسْتَقَرُّ (12) zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake |
يُنَبَّأُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ (13) Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar |
بَلِ الْإِنسَانُ عَلَىٰ نَفْسِهِ بَصِيرَةٌ (14) Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne |
وَلَوْ أَلْقَىٰ مَعَاذِيرَهُ (15) Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba) |
لَا تُحَرِّكْ بِهِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ (16) Kada ka mõtsar* da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni) |
إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ (17) Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa |
فَإِذَا قَرَأْنَاهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ (18) To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa |
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ (19) sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa |
كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ (20) A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne |
وَتَذَرُونَ الْآخِرَةَ (21) Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira) |
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ (22) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne |
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ (23) Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne |
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ بَاسِرَةٌ (24) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne |
تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ (25) Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso |
كَلَّا إِذَا بَلَغَتِ التَّرَاقِيَ (26) A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai |
وَقِيلَ مَنْ ۜ رَاقٍ (27) kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada |
وَظَنَّ أَنَّهُ الْفِرَاقُ (28) Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce |
وَالْتَفَّتِ السَّاقُ بِالسَّاقِ (29) Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri |
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمَسَاقُ (30) Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa* take |
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ (31) To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba |
وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ (32) Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya |
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰ أَهْلِهِ يَتَمَطَّىٰ (33) Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama |
أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ (34) Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa |
ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ (35) Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa |
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَن يُتْرَكَ سُدًى (36) Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi) |
أَلَمْ يَكُ نُطْفَةً مِّن مَّنِيٍّ يُمْنَىٰ (37) Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa) |
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ (38) Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa |
فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ (39) Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace |
أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَادِرٍ عَلَىٰ أَن يُحْيِيَ الْمَوْتَىٰ (40) Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu |