×

Surah Saba in Hausa

Quran Hausa ⮕ Surah Saba

Translation of the Meanings of Surah Saba in Hausa - الهوسا

The Quran in Hausa - Surah Saba translated into Hausa, Surah Saba in Hausa. We provide accurate translation of Surah Saba in Hausa - الهوسا, Verses 54 - Surah Number 34 - Page 428.

بسم الله الرحمن الرحيم

الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَلَهُ الْحَمْدُ فِي الْآخِرَةِ ۚ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْخَبِيرُ (1)
Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Yake abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã Nãsa ne, kuma shĩ ne Mai hikima, Mai labartawa
يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا ۚ وَهُوَ الرَّحِيمُ الْغَفُورُ (2)
Yã san abin da yake shiga a cikin ƙasã da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin ƙai, Mai gãfara
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَا تَأْتِينَا السَّاعَةُ ۖ قُلْ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتَأْتِيَنَّكُمْ عَالِمِ الْغَيْبِ ۖ لَا يَعْزُبُ عَنْهُ مِثْقَالُ ذَرَّةٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ وَلَا أَصْغَرُ مِن ذَٰلِكَ وَلَا أَكْبَرُ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ (3)
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra bã ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bã ta nĩsanta a cikin ƙasã, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin Littãfi bayyananne
لِّيَجْزِيَ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ۚ أُولَٰئِكَ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ (4)
Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata gãfara da wani arziki mai karimci
وَالَّذِينَ سَعَوْا فِي آيَاتِنَا مُعَاجِزِينَ أُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مِّن رِّجْزٍ أَلِيمٌ (5)
Kuma waɗanda suka yi mãkirci ga ãyõyin Mu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗannan sunã da wata azãba daga azãba mai raɗaɗi
وَيَرَى الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ الَّذِي أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ هُوَ الْحَقَّ وَيَهْدِي إِلَىٰ صِرَاطِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ (6)
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi sunã ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yanã shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwãyi, Gõdadde
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا هَلْ نَدُلُّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ يُنَبِّئُكُمْ إِذَا مُزِّقْتُمْ كُلَّ مُمَزَّقٍ إِنَّكُمْ لَفِي خَلْقٍ جَدِيدٍ (7)
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas, kunã a cikin wata halitta sãbuwa
أَفْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا أَم بِهِ جِنَّةٌ ۗ بَلِ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ فِي الْعَذَابِ وَالضَّلَالِ الْبَعِيدِ (8)
Ya ƙãga ƙarya ga Allah ne kõ kuwa akwai wata hauka a gare shi?" Ã'a, waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba, sunã a cikin azãba da ɓãta mai nĩsa
أَفَلَمْ يَرَوْا إِلَىٰ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُم مِّنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۚ إِن نَّشَأْ نَخْسِفْ بِهِمُ الْأَرْضَ أَوْ نُسْقِطْ عَلَيْهِمْ كِسَفًا مِّنَ السَّمَاءِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِّكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ (9)
Ashe fa, ba su yi dũbi ba zuwa ga abin da ke a gaba gare su da abin da ke a bãyansu daga sama da ƙasã? idan Mun so, sai Mu shãfe ƙasã da su, kõ kuma Mu kãyar da wani ɓaɓɓake daga sama a kansu. Lalle, a cikin wancan akwai ãyã ga dukan bãwã mai maida al'amarinsa ga Allah
۞ وَلَقَدْ آتَيْنَا دَاوُودَ مِنَّا فَضْلًا ۖ يَا جِبَالُ أَوِّبِي مَعَهُ وَالطَّيْرَ ۖ وَأَلَنَّا لَهُ الْحَدِيدَ (10)
Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda wata falala dagagare Mu. Yã duwatsu, ku konkõma sautin tasbihi tãre da shi kuma da tsuntsãye. Kuma Muka tausasa masa baƙin ƙarfe
أَنِ اعْمَلْ سَابِغَاتٍ وَقَدِّرْ فِي السَّرْدِ ۖ وَاعْمَلُوا صَالِحًا ۖ إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ (11)
Ka aikata sulkuna kuma ka ƙaddara lissãfi ga tsãrawa, kuma ka aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩ Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa
وَلِسُلَيْمَانَ الرِّيحَ غُدُوُّهَا شَهْرٌ وَرَوَاحُهَا شَهْرٌ ۖ وَأَسَلْنَا لَهُ عَيْنَ الْقِطْرِ ۖ وَمِنَ الْجِنِّ مَن يَعْمَلُ بَيْنَ يَدَيْهِ بِإِذْنِ رَبِّهِ ۖ وَمَن يَزِغْ مِنْهُمْ عَنْ أَمْرِنَا نُذِقْهُ مِنْ عَذَابِ السَّعِيرِ (12)
Kuma ga Sulaimãn, Mun hõre masa iska, tafiyarta ta safiya daidai da wata, kuma ta maraice daidai da wata. Kuma Muka gudãnar masa da marmaron gaci, kuma daga aljannu (Muka hõre masa) waɗanda ke aiki a gaba gare shi, da iznin Ubangijinsa. Wanda ya karkata daga cikinsu, daga umurnin Mu, sai Mu ɗanɗana masa daga azãbar sa'ĩr
يَعْمَلُونَ لَهُ مَا يَشَاءُ مِن مَّحَارِيبَ وَتَمَاثِيلَ وَجِفَانٍ كَالْجَوَابِ وَقُدُورٍ رَّاسِيَاتٍ ۚ اعْمَلُوا آلَ دَاوُودَ شُكْرًا ۚ وَقَلِيلٌ مِّنْ عِبَادِيَ الشَّكُورُ (13)
Sunã aikata masa abin da yake so, na masallatai da mutummutumai da akussa kamar kududdufai, da tukwãne kafaffu. Ku aikata gõdiya, yã ɗiyan Dãwũda, kuma kaɗan ne mai gõdiya daga bãyĩ Na
فَلَمَّا قَضَيْنَا عَلَيْهِ الْمَوْتَ مَا دَلَّهُمْ عَلَىٰ مَوْتِهِ إِلَّا دَابَّةُ الْأَرْضِ تَأْكُلُ مِنسَأَتَهُ ۖ فَلَمَّا خَرَّ تَبَيَّنَتِ الْجِنُّ أَن لَّوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ الْغَيْبَ مَا لَبِثُوا فِي الْعَذَابِ الْمُهِينِ (14)
Sa'an nan a lõkacin da Muka hukunta mutuwa a kansa bãbu abin da ya ja hankalinsu, a kan mutuwarsa, fãce dabbar ƙasa (gara) wadda take cin sandarsa. To a lõkacin da ya fãɗi, sai aljannu suka bayyana (ga mutãne) cẽwa dã sun kasance sun san gaibi, dã ba su zauna ba a cikin azãba mai wulãkantarwa
لَقَدْ كَانَ لِسَبَإٍ فِي مَسْكَنِهِمْ آيَةٌ ۖ جَنَّتَانِ عَن يَمِينٍ وَشِمَالٍ ۖ كُلُوا مِن رِّزْقِ رَبِّكُمْ وَاشْكُرُوا لَهُ ۚ بَلْدَةٌ طَيِّبَةٌ وَرَبٌّ غَفُورٌ (15)
Lalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa* a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara
فَأَعْرَضُوا فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ سَيْلَ الْعَرِمِ وَبَدَّلْنَاهُم بِجَنَّتَيْهِمْ جَنَّتَيْنِ ذَوَاتَيْ أُكُلٍ خَمْطٍ وَأَثْلٍ وَشَيْءٍ مِّن سِدْرٍ قَلِيلٍ (16)
Sai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan: talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan
ذَٰلِكَ جَزَيْنَاهُم بِمَا كَفَرُوا ۖ وَهَلْ نُجَازِي إِلَّا الْكَفُورَ (17)
Wancan, da shi Muka yi musu sakamako sabõda kãfircinsu. Kuma lalle, bã Mu yi wa kõwa* irin wannan sakamako, fãce kafirai
وَجَعَلْنَا بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ الْقُرَى الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا قُرًى ظَاهِرَةً وَقَدَّرْنَا فِيهَا السَّيْرَ ۖ سِيرُوا فِيهَا لَيَالِيَ وَأَيَّامًا آمِنِينَ (18)
Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin* garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu
فَقَالُوا رَبَّنَا بَاعِدْ بَيْنَ أَسْفَارِنَا وَظَلَمُوا أَنفُسَهُمْ فَجَعَلْنَاهُمْ أَحَادِيثَ وَمَزَّقْنَاهُمْ كُلَّ مُمَزَّقٍ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ (19)
Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce* su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya
وَلَقَدْ صَدَّقَ عَلَيْهِمْ إِبْلِيسُ ظَنَّهُ فَاتَّبَعُوهُ إِلَّا فَرِيقًا مِّنَ الْمُؤْمِنِينَ (20)
Kuma lalle, haƙĩƙa, Iblĩs ya gaskata zatonsa a kansu, sai suka bi shi fãce wani ɓangare na mũminai
وَمَا كَانَ لَهُ عَلَيْهِم مِّن سُلْطَانٍ إِلَّا لِنَعْلَمَ مَن يُؤْمِنُ بِالْآخِرَةِ مِمَّنْ هُوَ مِنْهَا فِي شَكٍّ ۗ وَرَبُّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ حَفِيظٌ (21)
Kuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kõme, Mai tsaro ne
قُلِ ادْعُوا الَّذِينَ زَعَمْتُم مِّن دُونِ اللَّهِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ وَمَا لَهُمْ فِيهِمَا مِن شِرْكٍ وَمَا لَهُ مِنْهُم مِّن ظَهِيرٍ (22)
Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su
وَلَا تَنفَعُ الشَّفَاعَةُ عِندَهُ إِلَّا لِمَنْ أَذِنَ لَهُ ۚ حَتَّىٰ إِذَا فُزِّعَ عَن قُلُوبِهِمْ قَالُوا مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ ۖ قَالُوا الْحَقَّ ۖ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ (23)
Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurin Sa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye* tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma
۞ قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ قُلِ اللَّهُ ۖ وَإِنَّا أَوْ إِيَّاكُمْ لَعَلَىٰ هُدًى أَوْ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ (24)
Ka ce: "Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya
قُل لَّا تُسْأَلُونَ عَمَّا أَجْرَمْنَا وَلَا نُسْأَلُ عَمَّا تَعْمَلُونَ (25)
Ka ce: "Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba
قُلْ يَجْمَعُ بَيْنَنَا رَبُّنَا ثُمَّ يَفْتَحُ بَيْنَنَا بِالْحَقِّ وَهُوَ الْفَتَّاحُ الْعَلِيمُ (26)
Ka ce: "Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani
قُلْ أَرُونِيَ الَّذِينَ أَلْحَقْتُم بِهِ شُرَكَاءَ ۖ كَلَّا ۚ بَلْ هُوَ اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (27)
Ka ce: "Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا كَافَّةً لِّلنَّاسِ بَشِيرًا وَنَذِيرًا وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ (28)
Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (29)
Sunã cẽwa, "Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya
قُل لَّكُم مِّيعَادُ يَوْمٍ لَّا تَسْتَأْخِرُونَ عَنْهُ سَاعَةً وَلَا تَسْتَقْدِمُونَ (30)
Ka ce: "Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَن نُّؤْمِنَ بِهَٰذَا الْقُرْآنِ وَلَا بِالَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ ۗ وَلَوْ تَرَىٰ إِذِ الظَّالِمُونَ مَوْقُوفُونَ عِندَ رَبِّهِمْ يَرْجِعُ بَعْضُهُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ الْقَوْلَ يَقُولُ الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا لَوْلَا أَنتُمْ لَكُنَّا مُؤْمِنِينَ (31)
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) "Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai
قَالَ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا لِلَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا أَنَحْنُ صَدَدْنَاكُمْ عَنِ الْهُدَىٰ بَعْدَ إِذْ جَاءَكُم ۖ بَلْ كُنتُم مُّجْرِمِينَ (32)
Makangara suka ce wa maraunana, "Ashe, mũ ne muka kange ku daga shiriya a bãyan ya zo muku? Ã, a' kun dai kasance mãsu laifi
وَقَالَ الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا بَلْ مَكْرُ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ إِذْ تَأْمُرُونَنَا أَن نَّكْفُرَ بِاللَّهِ وَنَجْعَلَ لَهُ أَندَادًا ۚ وَأَسَرُّوا النَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُا الْعَذَابَ وَجَعَلْنَا الْأَغْلَالَ فِي أَعْنَاقِ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ هَلْ يُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (33)
Kuma maraunana suka ce wa makangara. "Ã'a, (ku tuna) mãkircin dare da na rãna a lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan tãrayya." Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa
وَمَا أَرْسَلْنَا فِي قَرْيَةٍ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَا إِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُم بِهِ كَافِرُونَ (34)
Kuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya fãce mani'imtanta (shũgabanni) sunce, "Lalle mũ, mãsu kãfirta ne da abin da aka aiko ku da shi
وَقَالُوا نَحْنُ أَكْثَرُ أَمْوَالًا وَأَوْلَادًا وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ (35)
Kuma suka ce: "Mũ ne mafiya yawa ga dũkiya da ɗiya, kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba
قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ (36)
Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfiɗa arziki ga wanda Ya so, kuma Yanã ƙuntatãwa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba
وَمَا أَمْوَالُكُمْ وَلَا أَوْلَادُكُم بِالَّتِي تُقَرِّبُكُمْ عِندَنَا زُلْفَىٰ إِلَّا مَنْ آمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ لَهُمْ جَزَاءُ الضِّعْفِ بِمَا عَمِلُوا وَهُمْ فِي الْغُرُفَاتِ آمِنُونَ (37)
Kuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙãmi fãce wanda, ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan sunã da sakamakon ninkawa sabõda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin bẽnãye
وَالَّذِينَ يَسْعَوْنَ فِي آيَاتِنَا مُعَاجِزِينَ أُولَٰئِكَ فِي الْعَذَابِ مُحْضَرُونَ (38)
Kuma waɗanda suke mãkirci a cikin ãyõyinMu, sunã nẽman gajiyarwa, waɗannan abin halartãwa ne a cikin azãba
قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَيَقْدِرُ لَهُ ۚ وَمَا أَنفَقْتُم مِّن شَيْءٍ فَهُوَ يُخْلِفُهُ ۖ وَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ (39)
Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa, kuma Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa
وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ جَمِيعًا ثُمَّ يَقُولُ لِلْمَلَائِكَةِ أَهَٰؤُلَاءِ إِيَّاكُمْ كَانُوا يَعْبُدُونَ (40)
Kuma rãnar da Allah Ya ke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Malã'iku, "Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sunã bauta wa
قَالُوا سُبْحَانَكَ أَنتَ وَلِيُّنَا مِن دُونِهِم ۖ بَلْ كَانُوا يَعْبُدُونَ الْجِنَّ ۖ أَكْثَرُهُم بِهِم مُّؤْمِنُونَ (41)
Sukace: "Tsarki ya tabbata a gare Ka. Kai ne Majiɓincinmu, bã su ba. Ã'a, sun kasance sunã bauta wa aljannu. Mafi yawansu, da sũ suka yi ĩmani
فَالْيَوْمَ لَا يَمْلِكُ بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ نَّفْعًا وَلَا ضَرًّا وَنَقُولُ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا ذُوقُوا عَذَابَ النَّارِ الَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ (42)
Sabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wutã wadda "kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ قَالُوا مَا هَٰذَا إِلَّا رَجُلٌ يُرِيدُ أَن يَصُدَّكُمْ عَمَّا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُكُمْ وَقَالُوا مَا هَٰذَا إِلَّا إِفْكٌ مُّفْتَرًى ۚ وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُمْ إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ (43)
Kuma idan an karanta ãyõyin Mu bayyanannu a kansu, sai su ce: "Wannan bai zama ba fãce namiji ne yanã son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sunã bauta wa." Kuma su ce: "Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya da aka ƙãga." Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: ga gaskiya a lõkacin da ta je musu: "Wannan bã kõme ba fãce sihiri ne bayyananne
وَمَا آتَيْنَاهُم مِّن كُتُبٍ يَدْرُسُونَهَا ۖ وَمَا أَرْسَلْنَا إِلَيْهِمْ قَبْلَكَ مِن نَّذِيرٍ (44)
Kuma ba Mu bã su waɗansu littattafai ba waɗanda suke karãtun su, kuma ba Mu aika wani mai gargaɗi ba zuwa gare su a gabãninka
وَكَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ وَمَا بَلَغُوا مِعْشَارَ مَا آتَيْنَاهُمْ فَكَذَّبُوا رُسُلِي ۖ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ (45)
Kuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata, alhãli kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata Manzanni Na! To, yãya musũ Na (ga maƙaryata) ya kasance
۞ قُلْ إِنَّمَا أَعِظُكُم بِوَاحِدَةٍ ۖ أَن تَقُومُوا لِلَّهِ مَثْنَىٰ وَفُرَادَىٰ ثُمَّ تَتَفَكَّرُوا ۚ مَا بِصَاحِبِكُم مِّن جِنَّةٍ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا نَذِيرٌ لَّكُم بَيْنَ يَدَيْ عَذَابٍ شَدِيدٍ (46)
Ka ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dõmin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunãni, bãbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azãba mai tsanani
قُلْ مَا سَأَلْتُكُم مِّنْ أَجْرٍ فَهُوَ لَكُمْ ۖ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى اللَّهِ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ (47)
Ka ce: "Abin da na rõƙe ku na wani sakamako, to, amfãninsa nãku ne. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma shi Ma shadai ne a kan dukan kõme
قُلْ إِنَّ رَبِّي يَقْذِفُ بِالْحَقِّ عَلَّامُ الْغُيُوبِ (48)
Ka ce: "Lalle Ubangijina Yanã jẽfa gaskiya. (Shi) Masanin abũbuwan fake ne
قُلْ جَاءَ الْحَقُّ وَمَا يُبْدِئُ الْبَاطِلُ وَمَا يُعِيدُ (49)
Ka ce: "Gaskiya ta zo, kuma ƙarya bã ta iya fara (kome) kuma bã ta iya mayarwa
قُلْ إِن ضَلَلْتُ فَإِنَّمَا أَضِلُّ عَلَىٰ نَفْسِي ۖ وَإِنِ اهْتَدَيْتُ فَبِمَا يُوحِي إِلَيَّ رَبِّي ۚ إِنَّهُ سَمِيعٌ قَرِيبٌ (50)
Ka ce: "Idan na ɓace, to, inã ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, sabõda abin da Ubangijina Yake yõwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai ji ne, Makusanci
وَلَوْ تَرَىٰ إِذْ فَزِعُوا فَلَا فَوْتَ وَأُخِذُوا مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ (51)
Kuma dã kã gani, a lõkacin da suka firgita, to, bãbu kuɓuta, kuma aka kãma su daga wuri makusanci
وَقَالُوا آمَنَّا بِهِ وَأَنَّىٰ لَهُمُ التَّنَاوُشُ مِن مَّكَانٍ بَعِيدٍ (52)
Kuma suka ce: "Mun yi ĩmãni da Shi." To inã zã su sãmu kãmãwa daga wuri mai nisa
وَقَدْ كَفَرُوا بِهِ مِن قَبْلُ ۖ وَيَقْذِفُونَ بِالْغَيْبِ مِن مَّكَانٍ بَعِيدٍ (53)
Kuma lalle sun kãfirta da Shi a gabãnin haka, kuma sunã jĩfa da jãhilci daga wuri mai nĩsa
وَحِيلَ بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ مَا يَشْتَهُونَ كَمَا فُعِلَ بِأَشْيَاعِهِم مِّن قَبْلُ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا فِي شَكٍّ مُّرِيبٍ (54)
Kuma an shãmakance a tsakãninsu da tsakãnin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyõyinsu a gabãninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka mai sanya kõkanto
❮ Previous Next ❯

Surahs from Quran :

1- Fatiha2- Baqarah
3- Al Imran4- Nisa
5- Maidah6- Anam
7- Araf8- Anfal
9- Tawbah10- Yunus
11- Hud12- Yusuf
13- Raad14- Ibrahim
15- Hijr16- Nahl
17- Al Isra18- Kahf
19- Maryam20- TaHa
21- Anbiya22- Hajj
23- Muminun24- An Nur
25- Furqan26- Shuara
27- Naml28- Qasas
29- Ankabut30- Rum
31- Luqman32- Sajdah
33- Ahzab34- Saba
35- Fatir36- Yasin
37- Assaaffat38- Sad
39- Zumar40- Ghafir
41- Fussilat42- shura
43- Zukhruf44- Ad Dukhaan
45- Jathiyah46- Ahqaf
47- Muhammad48- Al Fath
49- Hujurat50- Qaf
51- zariyat52- Tur
53- Najm54- Al Qamar
55- Rahman56- Waqiah
57- Hadid58- Mujadilah
59- Al Hashr60- Mumtahina
61- Saff62- Jumuah
63- Munafiqun64- Taghabun
65- Talaq66- Tahrim
67- Mulk68- Qalam
69- Al-Haqqah70- Maarij
71- Nuh72- Jinn
73- Muzammil74- Muddathir
75- Qiyamah76- Insan
77- Mursalat78- An Naba
79- Naziat80- Abasa
81- Takwir82- Infitar
83- Mutaffifin84- Inshiqaq
85- Buruj86- Tariq
87- Al Ala88- Ghashiya
89- Fajr90- Al Balad
91- Shams92- Lail
93- Duha94- Sharh
95- Tin96- Al Alaq
97- Qadr98- Bayyinah
99- Zalzalah100- Adiyat
101- Qariah102- Takathur
103- Al Asr104- Humazah
105- Al Fil106- Quraysh
107- Maun108- Kawthar
109- Kafirun110- Nasr
111- Masad112- Ikhlas
113- Falaq114- An Nas